Yajin Aiki: Ƴan Kwadago Sun Dira Ofishin SGF a Abuja, Za a Sa Labule da Jiga Jigan Gwamnati

Yajin Aiki: Ƴan Kwadago Sun Dira Ofishin SGF a Abuja, Za a Sa Labule da Jiga Jigan Gwamnati

  • Jagororin ƴan kwadago sun isa ofishin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume domin sa labule da wasu ƙusoshin kasar
  • Sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ne ya kira zaman domin kawo ƙarshen yajin aikin da ma'aikatan suka fara yau Litinin, 3 ga watan Yuni
  • Wata majiya ta ce wannan zama ne zai tantance ci gaba ko janye yajin aikin da aka fara kan mafi ƙarancin albashi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tawagar wakilan ƙungiyoyin kwadago a Najeriya sun isa ofishin sakataren gwamnatin tarayya a birnin Abuja yau Litinin, 3 ga watan Yuni.

Wata majiya ta bayyana cewa shugabannin ƴan kwadagon sun isa ofishin ne domin sa labule da wasu manyan jami'an gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Sojoji sun kewaye wurin taron ƴan kwadago da ƙusoshin gwamnati a Abuja

Shugabannin NLC da TUC.
Jagororin ma'aikata sun amsa gayyata, sun isa ofishin sakataren gwamnatin tarayya Hoto: Nigeria Labour Congress
Asali: Twitter

Majiyar ta shaidawa jaridar Punch cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu gana da wakilan gwamnatin tarayya a ofishin SGF, yanzu haka wakilan ƴan kwadago sun samu wuri sun zauna suna jiran karasowar su."

Sai dai majiyar ba ta bayyana sunayen wakilan gwamnatin da suka gayyato shugabannin kwadagon zuwa wannan taro ba.

Gwamnatin tarayya ta kira taro da NLC

Tun da farko dai The Nation ta kawo labari sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya gayyaci 'yan kwadago zuwa taron gaggawa.

Sanata Akume ya shirya taron ne da nufin kawo ƙarshen yajin aikin da ƴan kwadagon suka fara kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya (TUC), Kwamared Festus Osifo ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ranar Litinin, 3 ga watan Yuni.

Osifo ya ce shugabannin kwadagon da suka hada da jagororin NLC da TUC za su halarci zaman da aka gayyace su a ofishin SGF.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun bi umarnin kungiyoyin NLC da TUC

Kungiyar kwadago za ta janye yajin aiki?

Wata majiya ta bayyana cewa duk abin da aka tattauna a wannan zama shi ne zai yanke ko ƴan kwadagon za su janye ƴajin aikin da suka fara, wanda ya gigita Najeriya.

A ranar Litinin, yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka kira ya gurgunta ayyukan tattalin arziki a fadin kasar nan.

Sun yanke shawarar ɗaukar wannan matakin ne kan mafi ƙarancin albashi da kuma ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi wa ƴan rukunin Band A.

NLC: Yajin aiki ya kankama a Kano

A wani rahoton kuma ma'aikatan gwamnati a Kano sun yi zamansu a gida yayin da NLC ta ayyana shiga yajin aiki daga yau Litinin, 3 ga watan Yuni.

An kulle sakateriyar Audu Baƙo yayin da aka tsayar da duk wasu harkokin sufuri a filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Kano ban da jirgin alhazai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262