Gwamnatin Tinubu Ta Ɗauki Matakin Dakile Yajin Aikin Ƴan Kwadago, Ta Kira Taro

Gwamnatin Tinubu Ta Ɗauki Matakin Dakile Yajin Aikin Ƴan Kwadago, Ta Kira Taro

  • Yayin da yajin aiki ƴan kwadago ke ƙara kankama, gwamnatin tarayya ta kira taron kwamitin mafi ƙarancin albashi
  • Hukumar kula da albashi da kuɗin shiga ta ƙasa (NSIWC) ce ta kira taron wanda zai gudana ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024
  • NLC da TUC sun fice daga taron kwamitin wanda aka yi ranar 31 ga watan Mayu bayan gwamnati ta kafe kan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagoranci Bola Ahmed Tinubu ta kira taron kwamitin da aka kafa kan sabon mafi karancin albashi a Najeriya

Gwamnatin ta kira taron kwamitin ne ta hannun hukumar kula da albashi da kuɗaɗen shiga ta ƙasa (NSIWC).

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Abubuwan da aka Amince da su a taron Gwamnatin Tinubu da ƴan ƙwadago

Shugabannin NLC da Bola Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta kira taron kwamitin mafi ƙarancin albashi Hoto: NLC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Taron wanda ya ƙunshi kungiyoyin kwadago zai gudana ne idan Allah ya kaimu gobe Talata, 4 ga watan Yunin 2024, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin ya yi zaman ƙarshe ranar Jumu'a, 31 ga watan Mayu lokacin da ƴan kwadago suka tashi suka fice daga wurin taron tun gabanin a kammala.

Abin da ya jawo yajin aikin NLC

Ƴan kwadago sun fice daga taron ne saboda gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu sun kafe kan N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Bayan haka kuma ƴan kwadagon sun sanar da cewa za su fara yajin aikin sai baba-ta gani daga tsakar daren ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Ajaero da takwaransa na TUC, Festus Osifo suka fitar, sun nuna damuwa matuƙa kan gazawar gwamnatin tarayya na aiwatar da sabon albashi.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Sojoji sun kewaye wurin taron ƴan kwadago da ƙusoshin gwamnati a Abuja

Sun kuma bukaci gwamnatin tarayya ta soke karin kudin wutar lantarki wanda aka yiwa ƴan rukunin Band a A, Channels tv ta ruwaito.

Tun farko manyan kungiyoyin biyu sun bayar da wa'adin ranar 31 ga Mayu, 2024, a gama tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi amna abun ya ci tura.

Sojoji sun kewaye wurin taron NLC

A wani rahoton na daban NLC ta ankarar da cewa dakarun sojojin Najeriya sun kewaye wurin taron ƴan kwadago da wakilan gwamnatin tarayya.

Shugabannin kwadagon sun isa ofishin sakataren gwamnatin tarayya bayan an gayyace su zuwa taron gaggawa ranar Litinin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262