Yajin Aiki Ya Jawo Kungiyoyin Kwadago Sun Kulle Majalisar Tarayya a Abuja

Yajin Aiki Ya Jawo Kungiyoyin Kwadago Sun Kulle Majalisar Tarayya a Abuja

  • Ƙungiyoyin ƙwadago a faɗin Najeriya sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a ranar Litinin, ga watan Yunin 2024
  • Yajin aikin ya kawo tsaiko inda abubuwa da dama suka tsaya cak yayin da sauran ƙungiyoyin suka shiga yajin aikin na ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC
  • Majalisa da sakatariyar gwamnatin tarayya na daga cikin wuraren da aka kulle domin bin umarnin ƙungiyoyin ƙwadagon kan shiga yajin aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kungiyar ma’aikatan majalisar tarayyar Najeriya (PASAN) ta tsunduma cikin yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara a faɗin Najeriya.

Ma'aikatan ƙungiyar sun kulle majalisar tarayya domin bin umarnin ƙungiyoyin ƙwadago na shiga cikin yajin aikin.

Kara karanta wannan

ASUU ta bayyana matsayarta kan shiga yajin aikin kungiyoyin kwadago

An kulle majalisar tarayya saboda yajin aiki
Kungiyoyin kwadago na ci gaba da yajin aiki a Najeriya Hoto: Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Yajin aiki ya sa an kulle majalisar tarayya

Ƙungiyar ta rufe ƙofofi biyu na harabar majalisar inda ma’aikata da sauran masu son zuwa majalisar suka kasa samun damar shiga, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta kuma datse wutar lantarki da ruwan sha ga gine-gine biyu na majalisar dattawa da ta wakilai da kuma sauran ofisoshi a harabar, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Wasu ma’aikatan agaji a harabar da suka je bakin aiki ba su samu damar shiga ba, yayin da aka ga jami’an ƙungiyar na ɗaukar matakin tabbatar da ana yin yajin aikin.

'Yan kwadago sun kulle sakatariyar gwamnati

Yajin aikin ya shafi sakatariyar gwamnatin tarayya, inda akwai ofisoshin ma'aikatun ƙwadago da samar da ayyukan yi, sadarwa, Neja Delta da sauransu.

A sakatariyar an ga shugabannin ƙungiyoyin na shige da fice domin tabbatar da cewa babu ma'aikacin da ke aiki a ofis.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: NLC ta kawo babban cikas a a kotu kan rigimar sarautar Kano

Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC dai sun fara yajin aikin ne bayan an kasa cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Yajin aiki: An kulle ƙofar ministan Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da ɗaukar zafi a babban birnin tarayya Abuja.

Ƙungiyoyin ƙwadago sun rufe babbar kofar ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja wadda aka fi sani da kofar Minista, inda a ka hana ma’aikatan shiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng