Manyan Abubuwan da Suka Faru a Majalisar Dattawa a Makon da Ya Gabata

Manyan Abubuwan da Suka Faru a Majalisar Dattawa a Makon da Ya Gabata

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta fara gudanar da ayyukanta a ranar Litinin da ta gabata ta hanyar sauraron ra'ayoyin jama'a kan ƙudirin komawa amfani da tsohon taken Najeriya.

Kwamitocin majalisar dattawa kan harkokin shari’a, kare hakkin ɗan Adam da harkokin cikin gida ne suka shirya zaman sauraron jin ra'ayin jama'an.

Abubuwan da suka faru a majalisar dattawa
Majalisar dattawa ta amince da dawo da yin amfani da tsohon taken Najeriya Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta yi duba kan muhimman ayyukan da majalisar ta gudanar a makon da ya gabata.

Majalisa ta amince a sauya taken Najeriya

Majalisar dattawa a ranar Talata, 28 ga watan Mayu ta zartar da ƙudirin komawa amfani da tsohon taken Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Matawalle ya dauki zafi kan kisan sojoji a Abia, ya fadi matakin dauka

Ƙudirin zai maye gurbin taken da ake amfani da shi a yanzu da tsohon da aka fara amfani da shi a lokacin samun ƴancin kai a ranar, 1 ga watan Oktoban 1960.

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya daina amfani da tsohon taken na Najeriya a shekarar 1978.

Majalisa ta dawo da Sanata Abdul Ningi

Majalisar dattawa a ranar Talata ta janye dakatarwar da ta yiwa Sanata Abdul Ningi na jam'iyyar PDP, watanni biyu bayan an dakatar da shi saboda zargin da ya yi kan yin cushe a kasafin kuɗin shekarar 2024..

Majalisar dattawan ta sanar da dawo da Sanatan mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya ne bayan ta kammala wani zaman sirri wanda ya shafe kusan awa ɗaya.

Tinubu ya halarci zaman majalisa

A ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, majalisar dattawa da ta wakilai sun gudanar da wani zama na tare domin tunawa da shekaru 25 na mulkin dimokuradiyya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan APC 25, ta hana su ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa

Shugaba Tinubu, wanda ya yi sanata a jamhuriya ta uku, ya halarci zaman inda ya yi jawabi ga ƴan majalisun na kusan mintuna bakwai.

Wannan dai shi ne karo na biyu da shugaban ƙasan ya yi jawabi a zaman hadakar majalisun tarayya tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.

Lokacin farko da ya yi jawabi ga ƴan majalisun shi ne yayin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 a watan Nuwamba.

Shugabannin majalisa sun gana da ƴan ƙwadago

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin majalisar dokokin tarayya sun saka labule da 'yan kwadago domin yin wani taron gaggawa a daren yau.

Wannan ganawar na daga wani yunkurin da ƴan majalisar ke yi na ganin ƴan ƙwadago ba su shiga yajin aikin da suka dauri aniyar farawa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel