Jirgi Zai Daina Tashi Yayin da Kungiyoyin Sufurin Jiragen Sama Suka Shiga Yajin Aiki

Jirgi Zai Daina Tashi Yayin da Kungiyoyin Sufurin Jiragen Sama Suka Shiga Yajin Aiki

  • Ƙungiyoyin sufurin jiragen sama na Najeriya sun sanar da shirinsu na shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka fara
  • Ƙungiyoyin sun buƙaci mambobinsu da su janye gudanar da ayyukansu a dukkanin filayen tashi da saukar jiragen sama na Najeriya
  • Yajin aikin dai ya fara ne bayan ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnatin tarayya sun kasa cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi da janye tallafin lantarki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyoyin ma'aikatan sufurin jiragen sama na Najeriya sun shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara a faɗin Najeriya.

Ƙungiyoyin sun buƙaci dukkanin mambobinsu da su janye ayyukan da suke yi a faɗin filayen tashi da saukar jiragen sama a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gargadi ma'aikata ana dab da fara yajin aiki

Kungiyoyin sufurin jiragen sama sun fara yajin aiki
Kungiyoyin sufuri jiragen sama sun fara yajin aiki Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/Getty Images, NLC
Asali: Facebook

Ƙungiyoyin sufurin jirage sun shiga yajin aiki

Janyewar za ta fara aiki ne da ƙarfe 12:00 na safiyar ranar Litinin 3 ga watan Yuni, kamar yadda ƙungiyoyin suka bayyana, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyin sun hada data ma’aikatan sufurin jiragen sama ta ƙasa (NUATE), manyan ma’aikatan sufurin jiragen sama na Najeriya (ATSSSAN), ƙungiyar ƙwararrun ma’aikatan sufurin jiragen sama (ANAP) da ƙungiyar NAAPE.

Ƙungiyoyin sun ɗauki matakin ne bayan wani taron gaggawa da suka gudanar a ranar Lahadi, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Wane umarni ƙungiyoyin suka ba da?

Ƙungiyoyin a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar sun umarci dukkanin rassansu da su bi wannan umarnin.

Janye gudanar da ayyukan ƙungiyoyin a filin jiragen saman zai kasance ne na har sai abin da hali ya yi.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke magidanci kan siyar da diyarsa a N1.5m

"Domin bin umarnin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC, muna sanar da jama'a cewa mun shiga yajin aiki a faɗin ƙasar nan daga ranar, 3 ga watan Yunin 2024. Za a janye dukkanin ayyuka a filayen jiragen sama har sai abin da hali ya yi."
"Yajin aikin zai fara ne a ɓangaren tashin jiragen sama na ƙasa da ƙasa a ranar Talata, 4 ga watan Yunin 2024."
"Dukkanin ma'aikatan filayen jiragen sama ya kamata su fahimci muhimmancin wannan fafutukar. Dukkanin rassan ƙungiyoyin mu su tabbatar sun bi wannan umarnin a dukkanin filayen jiragen sama."

Gwamnati ta gargadi kungiyoyin ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta gargaɗi ma'aikata kan shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara a faɗin Najeriya.

Ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya bayyana cewa ma'aikatan da suka shiga yajin aikin za su iya fuskantar ɗauri a gidan kaso na watanni shida saboda ya saɓa doka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel