Karin Albashi: Rundunar ’Yan Sanda Ta Fitar da Bayanin da Zai Hana 'Yan Kwadago Yajin Aiki

Karin Albashi: Rundunar ’Yan Sanda Ta Fitar da Bayanin da Zai Hana 'Yan Kwadago Yajin Aiki

  • A yau Litinin, 3 ga watan Yuni kungiyar kwadago ta ayyana fara yajin aiki saboda kasa samun matsaya kan karin mafi ƙarancin albashi
  • Kungiyar ta yi zama da shugabannin majalisar tarayya kan neman mafita maimakon tafiya yakin aikin amma ba a samu matsaya ba
  • Rundunar yan sandan Najeriya ta tura sakon gargadi ga kungiyar kwadago kan yajin aikin da take farawa a safiyar yau Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - A yayin da kungiyar kwadago ke shirin fara yajin aiki a yau Litinin, 3 ga watan Yuni, rundunar yan sandan Najeriya ta tura mata gargadi.

Rundunar ta yi gargadin ne ganin zaman gaggawa da aka yi tsakanin kungiyar kwadago da shugabannin majalisun tarayya bai ba da fa'ida ba.

Kara karanta wannan

Manyan ayyukan da aka bukaci Bola Tinubu ya karasa a jihohin Arewa

Police IGP
Rundunar 'yan sanda ta bukaci dakatar da yajin aikin 'yan kwadago. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

A cikin sakon da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ta nuna cewa yakin aikin ya sabawa dokar kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yajin-aiki: Kira a bi dokar kasa

Rundunar yan sanda ta ce akwai bukatar kungiyar kwadago ta bi dokar kasa kan yajin aikin da take kokarin shiga.

Ta ce yajin aikin ya sabawa doka kuma aiwatar da shi zai kai ga rashin doka da oda a fadin Najeriya.

Rundunar har ila yau ta ce tafiya yakin aikin zai kai da karuwar matsalar rashin tsaro da kasar ke fama da ita cikin shekaru.

Buƙatar komawa teburin sulhu da NLC

Rundunar yan sandan Najeriya ta bukaci kungiyar kwadago ta koma teburin sulhu domin neman mafita ga ma'aikata.

Ta ce tafiya yajin aikin zai jefa ma'aikata cikin wahala maimakon sama musu sauki wajen gudanar da rayuwa.

Kara karanta wannan

Yajin aiki ya tabbata: An tashi taron NLC da majalisar tarayya ba tare da wata nasara ba

Kiran 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Rundunar ta yi kira ga yan kasa su cigaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum cikin lumana.

Ta kuma tabbatar da cewa za ta yi dukkan abin da ya kamata wajen tabbatar da tsaro a fadin Najeriya.

Minista ya yi kira ga yan kwadago

A wani rahoton, kun ji cewa ministan yada labarai na kasa, Idris Muhammad ya yi kira ga kungiyar kwadago kan shiga yajin aiki a yau Litinin.

Ministan ya ce lallai akwai bukatar kungiyar kwadago ta janye aniyarta na shiga yajin aiki tare da amincewa da kudin da gwamnati ta ayyana a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel