Bayan Kama G Fresh Al’ameen, Hisbah Ta Sake Kama Wani Fitaccen Dan TikTok a Kano
- Hukumar Hisbah a Kano ta cafke fitaccen jarumin TikTok, Rabi'u Sulaiman, wanda aka fi sani da Lawancy
- Hukumar ta kama Lawancy ne bisa zargin yana raye-raye na baɗala da kuma riƙe hannun mata a bidiyo
- Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da hukumar ta sanar da cewa ta kama fitaccen dan TikTok, G-Fresh Al'ameen
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Rahotannin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani fitaccen ɗan TikTok, Rabi'u Sulaiman.

Source: UGC
Rabi'u Sulaiman, wanda aka fi sani da Lawancy a duniyar TikTok, ya kware wajen rawar baɗala da 'yan mata tare da rike hannu.

Kara karanta wannan
Kano: Hukumar Hisbah ta kama fitaccen dan TikTok, G Fresh Al'ameen, an gano dalili
Hisbah ta kama Rabi'u Lawancy
Gidan rediyo na Freedom da ke Kano ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa hukumar Hisbah ta kama Lawancy a kokarin da take yi na tsaftace kafafen sada zumunta da ke da alaka da jihar.
Ko a shekarar 2023, hukumar ta taɓa cafke Lawancy kan yaɗa baɗala a abubuwan da ya ke ɗora a intanet amma ta yi masa afuwa bayan ya ce ya tuba.
Hisbah ta kama G-Fresh Al'ameen
Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da hukumar ta sanar da cewa ta kama fitaccen jarumin TikTok, kuma mawaki, G-Fresh Al'ameen.
Mun ruwaito cewa Hisbah ta kama G-Fresh ne saboda zargin ya yi izgili ga ayoyin Al-Kur'ani da kuma yaɗa baɗala.
Hukumar ta ce za ta gurfanar da G-Fresh Al'ameen a gaban kotu a gobe Litinin, 3 ga watan Yunin 2024.
Asali: Legit.ng