Janar Abdulsalami Ya Fadi Nadamarsa Kan Mika Mulki a Hannun Farar Hula
- Tsohon shugaban ƙasa Abdulsalami Abubakar ya yi magana kan cikar Najeriya shekara 25 a kan turbar mulkin dimokuraɗiyya
- Tsohon shugaban na mulkin soja ya bayyana cewa bai yi nadamar miƙa mulki a hannun farar hula ba a shekarar 1999
- Ya bayyana cewa duk da har yanzu ba a samu ci gaban da ake so ba, ƙasar nan tana kan turbar da ta dace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce ba ya nadamar mika mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na mulkin dimokuraɗiyya.
Abdulsalami Abubakar ya miƙa mulki ga tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a shekarar 1999, wanda hakan ya kawo ƙarshen mulkin soja.
Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da jaridar The Sun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace nadama Abdulsalami yake da ita?
Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa bai yi nadamar miƙa mulki hannun farar hula ba duk da cewa har yanzu ƙasar nan ba ta samu ci gaban da ya kamata ba.
"Aa ko kaɗan, ina farin ciki da abin da ke faruwa. Eh tabbas ba komai ba ne yake tafiya daidai, amma gamu a yau muna murnar cika shekara 25 da mulkin dimokuraɗiyya."
"Eh muna godiya ga Allah, sannan ina farin ciki cewa yanzu an yi shekara 25 da na miƙa mulki. Muna godiya ga Allah cewa Najeriya da ƴan Najeriya na cin gajiyar mulkin dimokuraɗiyya."
"Ba mu kai inda muke son zuwa ba, amma mun samu ci gaba tun daga shekarar 1999."
"Matsalar kawai da ake fuskanta da tsarin ita ce har yanzu mutane suna siyar da ƙuri'unsu, suna bari ƴan siyasa su yi amfani da su wajen sace akwatunan zaɓe da sauran abubuwan da ya kamata a ce mun daina yinsu a yanzu."
"Amma a hankali a hankali ƴan Najeriya fara gane gaskiya, sun fara gane cewa ƙuri'unsu na da amfani kuma suna tabbatar da cewa an ba su abin da suka zaɓa."
- Abdulsalami Abubakar
Abdulsalami ya faɗi masu hannu a juyin mulki
A wani labarin kuma, kun ji cewa Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya magantu kan juyin mulki a gwamnati.
Abdulsalami ya ce babu yadda za a yi nasarar juyin mulki ba tare da hadin kan ‘yan siyasa ba a kowace kasa.
Asali: Legit.ng