Lokaci Ya Yi: Kwamishinan Bauchi Ya Rasu Yana da Shekara 60 a Duniya
- Allah ya yiwa kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar Bauchi rasuwa a ranar Asabar, 1 ga watan Yunin 2024
- Ahmed Jalam ya rasu ne tare da direbansa a wani hatsarin mota da ya ritsa da su lokacin da yake kan hanyar zuwa garinsa na Jalam
- Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya aike da saƙon ta'aziyyarsa inda ya bayyana rasuwar kwamishinan a matsayin babban rashi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar Bauchi, Ahmed Jalam ya rasu.
Marigayin ya rasu ne tare da direbansa a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar babban titin Bauchi/Jalam a ranar Asabar, 1 ga watan Yunin 2024.
An bayyana cewa suna kan hanyarsu ta zuwa garin Jalam ne a ƙaramar hukumar Dambam a lokacin da hatsarin ya auku, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Bauchi ya yi ta'aziyya
Da yake miƙa saƙon ta'aziyyarsa, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar Ahmed Jalam a matsayin wani babban rashi.
Gwamnan ya bayyana cewa rasuwarsa ta bar giɓi saboda jajircewarsa wajen yiwa al'umma hidima, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
“Mutuwar kwamishinan ta bar babban giɓi a jihar kuma ta jefa mutanen jihar cikin alhini saboda yadda ya yi suna wajen sadaukar da kai da jajircewarsa wajen yin hidima."
"Ahmad Jalam ya riƙe muƙamin kwamishinan harkokin addini a shekarar 2019 kuma an sake naɗa shi matsayin kwamishina a shekarar 2023 kuma ya yi aiki a ma'aikatar ƙananan hukumomi da masarautu har zuwa ƙarshen rasuwarsa."
- Sanata Bala Mohammed
Kwamishinan ya rasu yana da shekaru 60 a duniya kuma ya bar mata da ƴaƴa.
Za a yi sallar jana’izarsa a safiyar ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garinsu na Jalam.
Wani Alhaji ya rasu a Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaya daga cikin alhazan jihar Legas mai suna, Idris Oloshogbo, ɗan kimanin shekaru 68 a duniya ya rasu a ƙasa mai tsarki.
Likitocin ƙasar Saudiyya ne suka tabbatar da rasuwar Alhaji Oloshogbo a birnin Makkah bayan ya dawo daga Ɗawafin Ka'abah.
Asali: Legit.ng