Rikicin Sarauta: 'Yan Sanda Sun Shiga Babban Ruɗani Kan Umarnin Kotu a Kano

Rikicin Sarauta: 'Yan Sanda Sun Shiga Babban Ruɗani Kan Umarnin Kotu a Kano

  • Ƴan sanda sun rasa umarnin da za su ɗauka yayin da kotuna biyar suka bayar da umarni masu cin karo da juna kan rikicin sarautar Kano
  • Kwamishinnan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya ce sun miƙa umarnin kotunan ga sufetan ƴan sanda na ƙasa
  • Ya ce a halin yanzun suna dakon ministan shari'a ya tuntuɓe su kan umarnin da ya dace su yiwa biyayya don magance lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta shiga cikin rudani kan yawan umarnin kotu da aka turo mata game da rikicin masarauta da ya dabaibaye jihar.

Rundunar ta ce umarnin kotun da ke cin karo da juna ya haifar da wani yanayi mai sarƙaƙiya saboda haka ta roƙi ƴan jarida su ba ta cikakken goyon baya.

Kara karanta wannan

Babu alamun warware rikicin sarautar Kano bayan ganawar Gwamna Abba da NSA

Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado
Rikicin Masarautar Kano: ‘Yan sanda sun shiga rudani kan umarnin kotu guda biyar Hoto: @Imranmuhdz
Asali: UGC

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Usaini Gumel ne ya yi wannan kiran yayin wani taro da shugabannin kungiyoyin kafafen yaɗa labarai a Kano jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abinda ya sa ƴan sanda a ruɗani

CP ya ce rundunar ta samu umarnin kotuna daban-daban guda biyar daga manyan kotunan tarayya da na jihohi dangane da rikicin sarautar, The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, tuni suka tura umarnin kotunan ga ministan shari'a domin samun ƙarin haske gabanin ɗaukar mataki na gaba.

"Na mika umarnin kotu guda biyar da suka shafi rikicin masarautar ga Sufeto Janar na ‘yan sanda wanda daga baya ya tuntubi Ministan Shari’a don yin karin haske da fassara.
"A halin yanzu muna jiran amsa game da wane umarni ya kamata mu bi saboda umarnin kotun sun ci karo da juna, kuma hakan y haifar da yanayi mai sarkakiya a jihar.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan APC 25, ta hana su ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa

"Da zarar mun sami fassarar da ya dace, za mu dauki matakin da ya kamata domin warware rikicin masarautar bisa ga tanadin doka."

- CP Usaini Gumel.

Bamu son yaɗa rahoton karya - Ƴan san da

Gumel ya koka kan yadda wasu gidajen rediyon ke yada rahotannin rashin da’a kan lamarin, rahoton Premium Times.

Kwamishinan ƴan sandan ya bukaci kafafen yada labarai da su tabbatar da gaskiyar labari tare da daidaita rahotannin su kafin yada su ga jama’a.

Ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su nemi karin haske daga ‘yan sanda kafin su buga rahotanni don tabbatar da an kaucewa ƙara ta’azzara lamarin.

Gwamna Abba da NSA sun gaza nemo mafita

A wani rahoton kuma ga dukkan alamu ganawar Gwamna Abba Kabir da Nuhu Ribaɗu ba ta lalubo hanyar warware rikicin sarautar Kano ba

Gwamna Abba ya ce ya ziyarci mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ne domin masa bayani kan halin da ake ciki a jiharsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262