Taken Najeriya: Tinubu Ya Yi Karin Haske Kan Hikimar Komawa Tsohon Taken Kasa

Taken Najeriya: Tinubu Ya Yi Karin Haske Kan Hikimar Komawa Tsohon Taken Kasa

  • A ranar Laraba, 29 ga watan Mayu shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan sabon taken Najeriya
  • Kudurin ya kawo suka sosai ga gwamnati ta inda mutane ke ganin ba shi ne muhimmin abu da ya kamata a maida hankali kai ba
  • Amma duk da haka shugaba Tinubu ya bayyana babban dalilin da ya sa shi canza taken kasar duk da halin da ake ciki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Duk da suka da yan kasa suka yi a kan sabon taken Najeriya da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo, shugaban kasar ya nuna ko gezau.

Bayan haka ya bayyana babban dalilin da ya sa shi canza taken kasar a daidai lokacin da kasar ke fama da matsin rayuwa da talauci.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarautar Kano, Ganduje ya sake roƙon ƴan Najeriya

Tinubu
Bola Tinubu ya yi magana kan muhimmancin sabon taken Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban kasar ya yi jawabin ne a jiya Alhamis yayin ganawa da kungiyar yan Arewa (ACF).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: "Muhimmancin canza taken Najeriya"

A yayin da yake zantawa da kungiyar ACF shugaba Bola Tinubu ya ce wasu za su tambaya ko canza taken yana da wani muhimmanci.

Ga amsar da ya bayar:

"Amsar da zan ba su ita ce, lallai canza taken abu ne mai matukar muhimmanci a gare mu, kuma tun da majalisa ta amince dole in rattaba hannu a kai"

-Bola Tinubu

Taken ya yi nuni da hadin kai

Shugaban kasar ya kara da cewa dole ne Najeriya ta fifita dukkan abin da zai kara taimaka mata wajen curewa wuri guda.

Saboda haka Mai girma Tinubu ya ce an dawo da taken ne domin yafi nuna hadewa da dunkulewar Najeriya wuri ɗaya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura sako ga shugabannin Arewa, tare da barazanar korar masu mukamai

Sabon taken dai shi ne wanda turawan mulkin mallaka suka kirkiro tun a karon farko kuma an cigaba da amfani da shi har zuwa 1978.

A shekarar 1978 lokacin da Cif Olusegun Obasanjo yake shugaban kasar mulkin mulkin soja, sai ya canza taken.

Gwamnati ta rufe hotel a sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Sokoto ta tabbatar da rufe Ifoma hotel bayan zarginsu da zama matattarar yada ayyukan barna a fadin jihar.

Har ila yau gwamnatin ta kara da cewa rufe hotel din ya biyo bayan kiraye-kiraye da suka samu daga mutanen garin Sokoto domin kawar da badala a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel