Kano: Tashin Hankali Yayin da Sarki Sanusi II da Aminu Ado Bayero Ke Shirin Sallar Jumu'a

Kano: Tashin Hankali Yayin da Sarki Sanusi II da Aminu Ado Bayero Ke Shirin Sallar Jumu'a

  • Mutane sun fara fargaba yayin da Sarki Muhammadu Sanusi II da Sarki na 15 Aminu Ado Bayero suka shirya yin Jumu'a babban masallacin fada
  • Damburan Kano ya sanar cewa Sanusi zai ja sallah yayin da Aminu Bayero ya sanar da shirinsa na zuwa masallacin fada domin yin Sallar Jumu'a
  • Har yanzun dai rundunar ƴan sandan jihar Kano ba ta ce komai ba kan lamarin wanda mutane ke tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Mutane sun fara fargaba da ɗar-ɗar yayin da ake sa ran mai martaba Sarkin Kano da aka mayar, Muhammadu Sanusi II zai jagoranci sallar Jumu'a a masallacin fada.

Kara karanta wannan

Masarautar Kano: Aminu Bayero zai jagoranci sallar Juma'a? 'Yan sanda sun magantu

Ana tsammanin Sanusi II zai yi limancin sallah raka'a biyu ta Jumu'a a babban masallacin Jumu'a na fadar sarki yau 31 ga watan Mayu, 2024.

Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.
Sarki Sanusi II da aka mayar da Aminu Ado na shirin zuwa Sallar Jumu'a a masallacin fada Hoto: @Imranmuhdz
Asali: UGC

Sarki Muhammadu Sanusi II zai yi limanci

Damburan Kano ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu da yammacin ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da Danburan Kano ya fitar ta gayyaci ɗaukacin al'ummar jihar su zo su saurari huɗubar Jumu'a da Sanusi III zai gabatar a masallacin fadar sarki.

Aminu Ado ya shirya zuwa masallacin fada?

Sai dai abin da ya sa mutane suka fara fargaba shi ne, Sarkin Kano na 15 da aka tsige, Aminu Ado Bayero, ya shirya yin sallar Jumu'a a masallacin fada.

A wata sanarwa da hadimin Aminu Ado ya fitar, ya gayyaci jama'a su biyo basaraken zuwa masallacin fada domin yin sallar Jumu'a yau.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: 'Yan majalisan Kano 12 sun yi mubaya'a ga Sarki na 15

Ya ƙara da cewa Aminu Ado Bayero zai fito ya kama hanyar zuwa babban masallacin Jumu'a na fada da misalin ƙarfe 12:30 na rana.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Har kawo yanzu hukumar ‘yan sanda ba ta ce uffan ba game da wannan lamari ɗa ke shirin faruwa wanda ka iya haɗa sarakunan biyu a wuri ɗaya.

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura saboda lambar wayarsa ba ta shiga ba.

Kauran Gwandu ya naɗa hakimai a Kebbi

A wani rahoton kun ji cewa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris Ƙauran Kwandu ya naɗa sababbin hakimai da dagattai 14 a wasu sassan jihar.

Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Garba Umar Dutsinmari ne ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Alhamis.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel