Dalibai Kusan 9,000 Suke Neman Bashin Kudin Karatu Duk Rana da Aka Bude Lamuni
- A ranar 24 ga watan Mayu gwamnatin tarayya ta ba daliban manyan makarantu damar fara cike fom ta yanar gizo domin neman lamuni
- Hukumar da ke lura da asusun lamunin (NELFUND) ta bayyana adadin daliban da suka yi rijista domin neman lamunin cikin mako daya
- Daraktan asusun ya kuma bayyana cewa kaso 90% na jami'o'in gwamnatin tarayya sun tura bayanan dalibansu ga hukumar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Asusun ba dalibai lamuni a Najeriya (NELFUND) ya bayyana adadin daliban da suka tura bayanansu domin neman lamuni cikin mako daya.
An bude kofar samun lamunin karatu
A ranar juma'a da ta wuce, 24 ga watan Mayu gwamnatin tarayya ta bude cika fom din neman lamunin karatu ta yanar gizo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton da jaridar Leadership ta wallafa ya nuna cewa an samu adadin dalibai sama da 60,000 da suke neman lamunin.
Makarantu sun tura bayanan dalibai
Daraktan hukumar ba da lamunin, Akintinde Sawyerr ya bayyana cewa a yanzu haka sun samu hadin kai daga manyan makarantun gwamnatin tarayya.
Ya ce a yanzu haka jami'o'i biyu ne da kwalejin kimiyya daya ba su tura bayanan daliban su ba amma suna fatan samun bayanan cikin kankanin lokaci.
Bayani kan daliban jami'o'in jihohi
Shugaban ya ce a yanzu an bude asusun ne ga dalibai da suke karatu a makarantun gwamantin tarayya, rahoton Vanguard.
Amma zuwa ranar 25 da wata mai kamawa za a ba dalibai da ke karatu a jami'o'in jihohi damar fara cika fam ta yanar gizo.
Mista Sawyerr ya ce tururuwan da daliban suka yi ya nuna tsananin bukata da ake da ita na ba da tallafi ga masu karatu a Najeriya.
Ba da lamunin karatu na cikin alkawuran da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a lokacin neman zabe a shekarar da ta wuce.
Tinubu ya nada shugaban NELFUND
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya nada wanda ya kafa bankin Zenith, Jim Ovia, a matsayin shugaban hukumar bayar da lamunin ilimi ta Najeriya.
Ovia zai yi aiki tukuru domin ganin cewa dalibai da matasan Najeriya sun sami ilimi mai zurfi da kwarewa a sana'a domin kawo cigaba ga kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng