Hanyoyin Samun Kudi Sun Yi Karanci Bayan Tafiyar El Rufai, An Samo Mafita a Kaduna
- Gwamnatin jihar Kaduna na fuskantar barazana kan karancin hanyoyin samun kuɗin shiga domin gudanar da ayyuka.
- Shugaban hukumar tattara haraji ta jihar, Jerry Adams ne ya bayyana haka yayin taron kaddamar da sababbin hanyoyin karɓar haraji
- Mista Jerry Adams ya bayyana yadda lamuran samar da kudin shiga suka ja baya biyo bayan masu matsaloli da jihar ta samu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Shugaban hukumar tattara kudin shiga ta jihar Kaduna, Jerry Adams ya bayyana cewa jihar tana cikin mawuyacin hali.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito mista Jerry Adams na cewa a halin yanzu hanyoyin samun kudin shiga sun toshe a jihar.
Saboda haka shugaban ya ce akwai bukatar karatun ta natsu domin samar da sababbin hanyoyi da kua tsuke aljihu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dabarar jihar Kaduna wajen bunkasa kudin shiga
Mista Jerry Adams ya bayyana cewa dole jihar za ta dauki mataki domin samar karin hanyoyyin samun kudin shiga.
A cewarsa, a yanzu haka gwamnatin ta kaddamar da tsarin tattara haraji ta yanar gizo inda za ta rika amfani da tsarin 'Project CRAFT' da "PAYKADUNA" domin tattara haraji cikin sauki.
Ya kara da cewa wannan tsarin zai taimaka wajen bunkasa harajin jihar, rage kashe kudi da gudanar da ayyuka domin inganta rayuwar mutanen jihar.
Mista Jerry Adams ya bayyana cewa kirkiro sababbin hanyoyin yana nuni da irin kokarin da gwamna Uba Sani ke yi wajen ciyar da jihar Kaduna gaba.
Yadda tattalin Kaduna ya ke a baya
A cewar Jerry Adams, a shekarun takwas da suka wuce jihar Kaduna ta samu karfin tattalin arziki da hanyoyin shigar kudi masu yawa.
Amma a yanzu abubuwa sun ja baya, an sayar da kadarorin gwamnati ga tarin bashi ya yiwa jihar yawa wanda ba ta iya gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
An kori shugabar APC a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan ikirarin Gwamna Uba Sani kan basukan jihar Kaduna, matsalar ta fara sauya salo.
Jam'iyyar APC a jihar ta dakatar da shugabar mata ta jam'iyyar a Kaduna bayan ta goyi bayan tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmed El-Rufai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng