Muhammadu Sanusi II Ya Zama Sabon Sarkin Kano a Hukumance, Bidiyo Ya Fito
- Muhammadu Sanusi II ya koma kan kujerar Sarkin Kano karo na biyu a hukumance yau Jumu'a, 24 ga watan Mayu, 2024
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa Sanusi takardar shaidar naɗa shi sarkin Kano a wani taro da aka shirya a gidan gwamnatin Kano
- Abba ya roƙi Sarkin ya tafiyar da mulki bisa tsarin addinin Musulunci kuma ya yi amfani da matsayinsa wajen haɗa kan masarauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano karo na biyu a hukumance.
Gwamnan ya miƙa sa Sarki Sanusi II takardar shaidar mayar da shi kan karagar sarautar a wani taro da aka shirya a fadar gwamnatin Kano yau Jumu'a.
Da yake jawabi a wurin taron naɗa sarkin, Gwamna Abba ya roki Sanusi II ya tafiyar da mulkinsa bisa tsarin addinin Musulunci, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun duba cancanta, amana da farin jinin Sarki wajen sake naɗa shi a karo na biyu. Ina kira ga sarki ya tafiyar da mulkinsa bisa koyarwar Musulunci.
"Ya kuma yi amfani da matsayinsa wajen hada kan masarauta, kuma ya samar da aminci da zaman lafiya tsakanin kungiyoyin Musulunci a wannan jiha.”
- Abba Kabir Yusuf.
Sarakuna sun halarci naɗin Sanusi II
Sarakunan gargajiya, masu naɗa sarki da manyan jami'an gwamnati sun halarci bikin naɗin sabon sarkin wanda aka yi a fadar gwamnatin Kano, The Cable ta tattaro.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan Gwamna Yusuf ya sanya hannu kan dokar masarautar Kano ta shekarar 2024 da majalisar dokoki ta amince da ita.
Sabuwar dokar dai ta maye gurbin dokar majalisar masarautun jihar Kano ta 2019, tare da rusa masarautun da Ganduje ya kafa.
Ganduje ya yi amfani da wannan doka wajen raba masarautar Kano zuwa gida biyar a watan Disamba 2019 tare da tsige Sanusi II, a ranar 9 ga Maris, 2020.
Wani jigon NNPP da ya je gidan Sarki a ranar ya ce sun yi farin da dawowar Sarki Sanusi saboda dalilai masu yawa.
Sanusi Isiyaku ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa duk wanda ka gani a Kano yana cikin farin ciki domin tun asali ƙarfin mulki aka sa aka canza Sarki ba wai don talaka ba.
"Mafi akasarin mutanen Kano sun ji daɗin wannan abu saboda ko a baya ƙarfin mulki aka nuna mana amma bawai al'umma, muna fatan Allah ya taimaki sarki ya ba shi ikon sauke nauyin talakawa," in ji shi.
Dattawa sun nuna damuwa da naɗin Sanusi
A wani rahoton kun ji cewa Dattawan Arewa sun nuna damuwa kan yadda ake ƙara samun yawaitar sauya sarakuna a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.
Kungiyar dattawan NEF ta buƙaci gwamnatin Kano da waɗanda abin ya shafa su tafiyar da batun dawo da Sanusi II cikin kulawa da kwarewa.
Asali: Legit.ng