Gwamnan PDP Ya Bi Dare Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 8, Ya Gargade Su

Gwamnan PDP Ya Bi Dare Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 8, Ya Gargade Su

  • Gwamna Siminilayi Fubara na jihar Rivers ya rantsar da sababbin kwamishinoni takwas da majalisar jihar ta tantance a baya
  • An gudanar da bikin rantsuwar ne a babban zauren gidan gwamnati da ke Port Harcourt a tsakiyar daren ranar Talatar nan
  • Gwamna Fubara ya bukaci sabbin kwamishinonin da aka nada da su fifita muradun jihar tare da kiyaye da'a a ayyukansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, ya rantsar da sababbin kwamishinoni takwas a matsayin mambobin majalisar zartarwa ta jihar (SEC).

An rantsar da kwamishinoni 8 a jihar Rivers
Gwamna Fubara ya rantsar da sabbin kwamishinoni 8 na jihar Rivers. Hoto: @Jmartinsijere
Asali: Twitter

Wannan ya biyo bayan tantancewar da majalisar dokokin jihar Rivers ta 10 ta yi wa wadanda gwamnan ya gabatar mata a matsayin kwamishinoni a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya maye gurbin kwamishinoni 8, ya tura sunaye ga majalisar dokoki

Abin da Fubara ya fadawa kwamishinonin

Gwamna Fubara ya umarce su da su dauki akidar adana sahihan bayanan yadda suke tafiyar da ayyukan ma’aikatunsu daban-daban, in ji rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da bikin rantsuwar ne a babban zauren gidan gwamnati da ke Port Harcourt a tsakiyar daren ranar Talata.

A yayin taron rantsuwar, Gwamna Fubara ya bukaci sababbin kwamishinonin da aka nada da su fifita muradun jihar tare da kiyaye da'a a cikin ayyukansu.

Ya kuma jaddada muhimmancin sadaukarwar su na yiwa al’ummar jihar Rivers hidima bisa gaskiya da jajircewa.

Jerin kwamishinonin da Fubara ya rantsar

Wani fitaccen ma'abocin shafin X, @Jmartinsijere ya wallafa sunayen sabbin kwamishinonin da aka rantsar da suka hada da:

1. Hon. Prince Charles O. Bekee

2. Mr. Collins Onunwo

3. Hon. Solomon Abel Eke

Kara karanta wannan

"Shekara 1 da na yi yafi 8 ɗinka a mulki": Gwamna ya sunce zanin mai gidansa a kasuwa

4. Sir Dr. Peter Medee

5. Hon. Olisaelloka Tasie-Amadi

6. Hon. Basoene Joshua Benibo

7. Mr. Tambari Sydney Gbara

8. Dr. Ovy Orluideye Chinendum Chukwuma

Kowane kwamishina yana da kwarewa da gogewa a aikin da aka ba shi, tare da yin alkawarin inganta harkokin mulki da ci gaban jihar Rivers.

Kwamishinoni 4 sun yi murabus a Rivers

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu kwamishinonin jihar Rivers hudu sun yi murabus daga mukaminsu a gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara.

Dukkanin kwamishinonin a cikin wasikar murabus dinsu sun bayyana cewa batutuwan da suka shafi rikicin siyasar da ya dade a jihar ne dalilin murabus din nasu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.