Caro White: Hukumar NAFDAC ta Gargadi Masu Shafa Man 'Bilicin' da Ya Shiga Gari
- Da alama masu amfani da mayukan kara hasken fata za su fuskanci barazana ga lafiyarsu bayan an gano daya daga mayukan na dauke da sinadarai masu illa
- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gargadi masu shafa man ‘bilicin’ mai suna Caro White da su daina domin an gano ya na da illa
- Takwarar NAFDAC a Turai ta RAPEX ce ta gano cewa man ya na da illoli sosai, saboda haka ne ma ta janye shi daga kasuwanninta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gargadi masu ta’ammali da man kara hasken fata mai matukar illa, Caro White.
Gargadin na zuwa ne bayan hukumar ta da ke sanya ido kan inganci kayayyaki a Turai ta RAPEX ta janye man bilicin din daga kasuwannin yankin.
Hukumar NAFDAC a sakon da ta wallafa a shafinta ta yi gargadin cewa man shafawar na dauke da sinadaran da za su iya illata jikin dan Adam.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Ku daina amfani da Caro White,’ NAFDAC
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta shawarci masu amfani da man kara hasken fata na Caro White su daina.
NAFDAC ta yi gargadin ne biyo bayan gano cewa akwai sinadarai masu illa ga lafiyan, kamar yadda Channels Televsion ta wallafa.
Ta ce duk da babu man a cikin abubuwan da hukumarsu ta haramta shigowa da su Najeriya, amma akwai bukatar a masu shigo da shi da masu rarraba shi a kasuwanni su bari.
Mata da dama har ma da maza ke amfani da samfurin mayukan kara hasken fata a wani kokari da su ke na karawa kansu kyan fata.
Likita ya fadi hadarin man haska fata
Kwararren Likita a asibitin Malam Aminu Kano (AKTH) Dr. Abdullahi Muhammad Atiku ya shaidawa Legit Hausa cewa akwai sinadaran da za su iya jawo cutar dajin fata idan ana amfani da mayukan kara haske.
A jawabinsa, likitan na ganin kara hasken fata ba shi ke nufin kara kyau ba, domin fatar kowane dan Adam da kyawunsa.
Ya shawarci al'umma, musamman mata da su yi hakuri da shafe-shafen mayukan kara hasken fata.
NAFDAC ta rufe gidajen 'pure water'
Mun ruwaito mu ku cewa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya ta garkame wasu gidajen ruwan leda da aka fi sani da 'pure water.'
Darakta-Janar na NAFDAC, Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa gidajen ruwa 27 aka rufe saboda su na samar da ruwa mara inganci da rashin tsafta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng