"Mu Taimaka Masu," Ganduje Ya Yi Magana Kan Mummunan Harin da Aka Kai Masallaci a Kano
- Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa waɗanda harin da aka kai masallaci ya shafa a jihar Kano ranar Laraba da ta gabata
- Shugaban APC na ƙasa ya buƙaci masu hannu da shuni su taimakawa iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda ke kwance suna jinya
- Tsohon gwamnan jihar Kano ya nuna damuwa matuƙa kan lamarin, inda ya yi addu'ar Allah ya bai wa waɗanda ke kwace a asibiti lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci masu hannu da shuni su taiimakawa iyalan waɗanda harin masallaci ya shafa a jihar Kano.
Dokta Ganduje, tsohon gwamnan Kano ya roƙi a taimakawa dangin mutanen ne yayin da yake miƙa sakon ta'aziyya ga dangin waɗanda suka rasa rayuwarsu.
Idan baku manta ba Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa harin ya zama ajalin mutum 15 kawo yanzu, yayin da wasu ke kwance a asibitin Murtala Muhammed.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ranar Laraba da ta wuce, Shafi’u Abubakar, ɗan shekara 38 ya watsa wa masallaci fetur, sannn ya cinna wuta a Larabar Abasawa a ƙaramar hukumar Gezawa.
The Nation ta ruwaito cewa mutane 32 ne a masallacin suna sallar asubahi lokacin da Shafi'u ya banka wutar saboda wani saɓani na rabon gado.
Ganduje ya nemi a tallafawa iyalansu
A wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu da kansa a Abuja ranar Asabar, Ganduje ya yi tir da harin kana ya miƙa sakon jaje ga waɗanda ibtila'in ya rutsa da su.
Tsohon gwamnan Kano ya nuna matuƙar damuwarsa kan mummunan lamarin da ya faru wanda ya zama ajalin masallata tare da addu'ar Allah ya tashi kafaɗun sauran da ke jinya.
A rahoton PM News, Ganduje ya ce:
"A lokuta irin waɗannan yana da muhimmanci mu taru don mu tallafa wa juna, mu jajantawa juna kuma mu karfafawa juna guiwa tare da tausayin mabukata.”
Shugaban APC ya bukaci kowa da kowa, musamman wadanda ke da rufin asiri da su taimakawa wadanda harin ya shafa kuma su kasance da su a irin wannan lokaci na jarabawa.
Kotu ta dakatar da bincikar Ganduje
A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta dakatar da bincikar tsohon Gwamna kuma shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje.
Tun da fari, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kafa wasu kwamitoci guda biyu domin binciken Ganduje kan zargin almundahana da rikicin siyasa.
Asali: Legit.ng