Ana Murnar Notcoin Ya Fashe, Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci Kan Jami'in Binance a Najeriya

Ana Murnar Notcoin Ya Fashe, Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci Kan Jami'in Binance a Najeriya

  • Babbar kotun tarayya ta yi watsi da buƙatar bayar da belin jami'in Binance, Tigran Gambaryan, saboda tunanin zai iya tserewa daga Najeriya
  • Mai shari'a Emeka Nwite ne ya yanke wannan hukunci yayin zaman ci gaba da shari'a kan tuhumar safarar kuɗin haram ranar Jumu'a a Abuja
  • Alƙalin ya amince da bayanan lauyan EFCC mai shigar da ƙara cewa idan aka bayar da belin zai iya sa ƙafa ya tsere saboda abin da ya faru a baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da buƙatar bayar da belin jami'in kamfanin hada-hadar kuɗin intanet watau Binance, Tigran Gambaryan.

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure tsakanin jami'an DSS da ma'aikata a zauren majalisar tarayya a Abuja

Jami'in kamfanin Binance na Najeriya, manhajar da ake hada-hadar kuɗin intanet da aka fi sani da Crypto na fuskantar shari'a kan tuhumar safarar kuɗin haram.

Jami'in Binance, Tigran Gambaryan.
Kotu ta yi watsi da buƙatar bayar da belin jami'in Binance a Najeriya Hoto: Binance
Asali: Facebook

Binance v Gwamnati: Kotu ta hana belin Gambaryan

A hukuncin da ya yanke ranar Juma’a, Mai shari’a Emeka Nwite ya ce akwai yiwuwar Gambaryan ya tsallake beli idan an sake shi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Nwite ya amince da jawabin lauyan masu shigar da ƙara cewa duba da tserewar ɗan uwan wanda ake tuhuma, da yiwuwar shi ma zai iya sa ƙafa ya gudu idan ya samu beli.

Idan ba ku manta ba, Nadeem Anjarwalla, shugaban kamfanin Binance na nahiyar Afroka, ya tsere daga wurin da ake tsare da shi a kwanakin baya.

EFCC ta nemi a hana belin Gambaryan

A jawabinsa lauyan hukumar EFCC, Ekele Iheanacho, ya ce bai kamata a bayar da belin wanda ake ƙara ba saboda zai iya barin Najeriya da zaran ya samu ƙofa.

Kara karanta wannan

Dala vs Naira: Dalilin da ya sa ya kamata Tinubu ya kori gwamnan CBN da minista 1

"Duk da fasfon wanda ake ƙara na hannun EFCC ba yana nufin zai ci gaba da zama a Najeriya bane saboda bayan kasancewarsa mazaunun Amurka, shi haifaffen ƙasar Armeniya ne," in ji Iheanacho.

Sakamakon haka Alkalin kotun ya yanke cewa duba da bayanan masu ƙara, bai kamata kotu ta amince da buƙatar belin Gambaryan ba.

Daga baya kuma ya ba da umarnin cewa a gaggauta gabatar da duk abin da ya shafi shari'ar domin kammala ta cikin lokaci, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

EFCC ta sake magana kan Crypto

A wani rahoton kuma hukumar EFCC ta ce ana amfani da wasu matasa da ke kasuwancin crypto wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya ba.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce 'yan ta'addan na amfani da irin su Binance wajen yin hada-hadar kudaden ayyukan ta’addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262