Band A: Ministan Makamashi Ya Bayyana Wadanda Suke Kuka Kan Karin Kudin Wuta

Band A: Ministan Makamashi Ya Bayyana Wadanda Suke Kuka Kan Karin Kudin Wuta

  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya caccaki masu sukar gwamantin tarayya kan karin kudin lantarki ga 'yan sahun Band A
  • Ministan ya ce maganar cewa karin kudin wutar ya jawo tashin kudin kayan masarufi magana ce da ba za ta kama hankali ba
  • Legit ta tattauna da wani mai saye da sayarwa, Muhammad Ibrahim domin domin jin yadda karin kudin wuta ya yi tasiri a harkokinsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Ministan makamashin Najeriya, Adebayo Adelabu ya ce masu kukan karin kudin wuta wadanda ba su biyan kudin ne a baya.

Power ministr
Ministan makamashi ya ce wadanda basu biyan kudin wuta ne masu kuka kan karin kudin lantarki. Hoto: Adebayo Adelabu
Asali: Facebook

Adebayo Adelabu ya bayyana haka ne biyo bayan kokawa da 'yan Najeriya ke yi kan karin kudin wuta ga 'yan layin Band A.

Kara karanta wannan

Atiku ya nemi takawa Bola Tinubu burki kan taba kudin ’yan fansho ayi ayyuka

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ministan yana cewa karin kudin ya kawo saukin kudaden da masu amfani da wuta suke kashewa wajen aiki da janareta da kashi 30% zuwa kashi 40%.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alakar kudin wuta da tsahin farashi

Har ila yau ministan ya karyata ikirarin da mutane ke yi wai karin kudin wutar ya kawo tashin farashin kayayyaki.

Dangane da 'yan layin Band A kuma, ya ce lallai idan za su yi lissafi da kyau za su ga sun samu sauki ne.

Musamman ma idan suka kwatanta kudaden da suke kashewa wurin sayan mai domin amfani da janareta.

Dalilin karin kudin shan wutan lantarki

Ministan ya ce karin kudin ba wai an kawo shi domin kara saka ƴan Najeriya cikin wahala bane, rahoton Pulse Nigeria.

Sai dai ma a cewarsa karin kudin zai zamo silar samun sauƙin rayuwa ne ga daukacin al'ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Kayayyaki za su kara tsada a Najeriya, an kara harajin shigo da kayan kasar waje

Su waye masu kukan karin kudin lantarki?

A karshe ministan yace saboda cigaban da aka samu bayan karin kudin waɗanda ba su biyan kudin wuta a baya ne kawai za su koka.

Ya kuma kara da cewa lallai abin takaici ne yadda Najeriya ta shekara 60 ba tare da samar da wutar lantarki ingantacciya ba.

Legit ta tattauna da Muhammad Ibrahim

Legit ta tattauna da wani mai harkar kasuwanci, Muhammad Ibrahim domin jin yadda karin kudin wuta ya yi tasiri a harkokinsu.

Muhammad ya zantawa Legit cewa lallai karin kudin wuta ya kara jawo tashin farshin kayayyakin da ake sarrafasu da wuta, kuma ya ce lamarin wuta bai inganta ba a Kano.

Dalilin da zai sa a rasa wuta a Najeriya

Har ila yau, kun ji cewa ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana irin masifar da Najeriya za ta shiga idan dai ba a kara kudin wuta ba.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya kalubalanci ‘yan majalisa a kawo hukuncin kashe barayin gwamnati

Adelabu ya ce nan da watanni uku wutar kasar gaba daya za ta dauke idan har ba a amince da karin kudin da hukumar ta yi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng