EFCC: Kotu Ta Bada Belin Emefiele Bayan Ya Ki Amincewa da Laifi

EFCC: Kotu Ta Bada Belin Emefiele Bayan Ya Ki Amincewa da Laifi

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a gaban kotu
  • Goodwin Emefiele bai amince da laifuffukan da ka zarge shi da su ba kuma lauyansa ya bukaci kotun ta bada belinsa
  • Kotun ta bada belin Emefiele a bisa N300m tare da kafa masa sharuddan da sai ya cika su kafin a sake shi daga gidan gyaran hali

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele a gaban kotu.

Emefiele
EFCC ta gurfanar da Emefiele kan canjin kudi. Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: UGC

Zargin da EFCC ke yi wa Emefiele

Hukumar tana zargin tsohon gwamnan ne da laifin amfani da N18.96b wajen buga kudade N684.5m.

Kara karanta wannan

Emefiele: Tsohon gwamnan CBN ya fara girbar abin da ya shuka wajen canjin kuɗi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikin zarge-zargen da hukumar ke yi wa tsohon gwamnan har da jefa yan Najeriya cikin firgici yayin canza kudi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin zaman kotun a yau Laraba Godwin Emefiele bai amince da laifin ba.

Lauya ya bukaci bada belin Emefiele

Bayan kin amincewa da laifuffukan da aka zargesa da su, lauyan Emefiele ya bukaci kotun ta bada belinsa.

Kotun ta bada belin tsohon gwamnan babban bankin tare da kafa masa sharudan, rahoton Daily Trust.

Sharuddan da kotu ta kafawa Emefiele

An bada belin Emefiele ne bisa zunzurutun kudi naira miliyan 300 da kawo waɗanda za su tsaya a maimakonsa mutum biyu.

Kotun shardanta cewa wadanda za su tsaya masan dole su kasance mazauna Najeriya kuma suna da kadarori a Maitama da ke Abuja.

An kuma kara shardanta cewa dole zai ajiye takardun tafiye-tafiyensa a gaban kotun ta inda ba zai yi tafiya zuwa kasar waje ba sai da izinin ta.

Kara karanta wannan

EFCC ta taso da batun canjin Naira na Buhari, za ta gurfanar da tsohon gwamnan CBN

Yaushe za a sake Emefiele?

Bayan bada belin, kotun ta yi umurni da a cigaba da tsare Emefiele a gidan gyaran hali da ke Kuje.

Za a cigaba da tsare Emefiele ne har zuwa lokacin da ya cika sharudan belin da kotun ta kafa masa. An kuma daga shari'ar zuwa ranar 28 da 29 da watan Mayu.

EFCC za ta kama Emefiele kan canjin kudi

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar EFCC ta taso da batun canjin takardun N200, N500 da N1000 wanda Godwin Emefiele ya jagoranta a mulkin Muhammadu Buhari.

EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) kan kashe N18.96bn wajen buga sabbin kuɗi na N684.5m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng