'Yan Sanda Sun Kama Yan Bindiga da Matsafi da Gashin Mutum
- Yan sandan jihar Delta sun kama wadanda ake zargi da garkuwa da mutane da dama tare da wasu matsafi a yankuna daban daban na jihar
- Ana zargin yan bindigar da aka kama da yawaita ayyukan ta'addanci a yankunan Warri, Ugheli, Sapele da sauran wurare a fadin jihar
- Kwamishinan yan sandan jihar, CP Abaniwonda Olufemi ya mika sako na musamman ga rundunar yan sandan kan aikin da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta -Rundunar ƴan sanda a jihar Delta sun sanar da kama ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da wasu matsafi dauke da gashin mutum.
'Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi
'Dan bindigar da aka fara kamawa mai suna Favour Eze, dan shekaru 24 ya fito ne daga ƙaramar hukumar Afikpo da ke jihar Ebonyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa an kama shi ne dauke da bindiga kirar gida da tarin kwayoyi da ya boye a cikin buhu.
Rahoton 'yan sanda ya nuna tuni aka tsare Favour Eze domin gudanar da bincike.
Yadda 'yan sanda suka kama yan bindigan
A wata nasara da yan sandan suka samu lokacin da suke sintiri a kan titin Ogwashi-Uku zuwa Kwale sun kama wata mota ja kirar Sienna.
Rahoton da jaridar Daily Post ta fitar ya nuna cewa an kama motar ne tana kokarin zuwa Warri daga Asaba.
Yan sanda sun kara kama 'miyagu'
A wani samame da rundunar ta kai wanda ASP Julius Robbinson ya jagoranta sun kama wani mutum dan shekaru 28 wanda dan asalin jihar Delta ne.
Binciken da aka gudanar kan mutumin ya jawo kama wani mutum mai shekaru 46 a wani otel dauke da bindiga.
Yayin da yan sanda suka tsananta bincike kan mutanen, an samu kama wani mutum mai shekaru 32 dauke da bindiga kirar AK47.
Sakamakon binciken 'yan sanda
Binciken da aka gudanar ya nuna ana zargin mutanen suna da hannu a kan garkuwa da mutane da ake a jihar Delta.
Ana zarginsu da garkuwa da mutane a yankunan Ugheli, Warri da Sapele kuma yanzu haka suna hannun hukuma.
Kwamishinan yan sandan jihar CP Abaniwonda Olufemi ya yabi rundunar'yan sandan bisa namijin ƙoƙarin da suka nuna.
Tare da haka ya kara da cewa za su cigaba da kokarin dakile ayyukan masu garkuwa da mutane da ƴan ta'adda a jihar.
Yan sanda sun kama dan bindiga a Neja
A wani rahoton, kun ji cewa dubun wani shugaban 'yan bindiga ya cika bayan da 'yan sanda suka kama shi a kasuwar Tungar Mallam da ke jihar Neja.
Kwamjshinan 'yan sanda na jihar Neja ya ce an kama dan bindigar mai suna Rabee bayan bin diddigin sa da tattara bayanan sirri da suka samu.
Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng