EFFC Ta Bayyana Sababbin Dabarun da ’Yan Yahoo Suka Kirkiro Wajen Damfara

EFFC Ta Bayyana Sababbin Dabarun da ’Yan Yahoo Suka Kirkiro Wajen Damfara

  • Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana sababbin hanyoyin da yan yahoo suka kirkiro
  • Daraktan hukumar ne na jihohin Edo, Delta da Ondo, Effa Okim ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kai wa ƴan jarida
  • A yayin ziyarar, mista Effa Okim ya kuma bayyana jihohin da suka fi yawan migyagu masu damfarar yanar gizo a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki kasa zagon kasa (EFFC) ta bayyana sababbin hanyoyin da masu damfarar yanar gizo da aka fi sani da 'yan yahoo suka fito da su.

Hukumar EFCC
EFCC za ta dakile sabuwar hanyar da 'yan yahoo suka fito da ita. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Hukumar ta ce ana samun karuwar yara masu kananan shekaru da suke shiga damfarar na amfani da bayanan da ba nasu ba domin rudar mutane.

Kara karanta wannan

'Ku ƙaura,' Gwamnati ta gargaɗi jihohi kan mummunar ambaliya

Dabarun da 'yan yahoo suka kirkiro

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa yaran suna kirkiro takardun haihuwa na bogi wurin bude asusun ajiya a bankuna domin samun daman gudanar da ayyukan damfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau yaran suna ƙoƙarin mallakar lasisin tuki na bogi domin samun samun damar ayyukan barna.

Daraktan hukumar a yankin jihohin Edo, Delta da Ondo, Effa Okim ne ya bayyana haka yayin da ya ziyarci ofishin ƙungiyar ƴan jarida a jihar Edo.

EFCC ta yi kira ga iyaye

A cewar mista Okim a mafi yawan lokuta idan aka kama yaran iyayensu na kokawa kan cewa 'yan kasa da shekaru 18 ne.

Saboda haka ne ya gargadi iyaye kan cewa duk wanda aka kama yana hadin baki da dansa wurin amfani da shekarun bogi zai fuskanci fushin hukuma.

Ya kara da cewa ana bukatar iyayen su bada gudunmawa wurin yaki da damfarar yanar gizo ba wai su rika taimakon 'ya'yansu a kai ba, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

An fayyace wanda ke rike da Najeriya bayan ficewar Tinubu da Kashim daga kasar

EFCC ta nemi hadaka da 'yan jarida

A kididdigar da hukumar EFCC ta fitar, jihar Edo ce ta biyu cikin jerengiyar jihohin da suka yi fice wurin masu damfarar yanar gizo.

Saboda haka ne hukumar ta kai wa ƴan jarida ziyara domin haɗaka wajen rage yawan ayyukan ta'addanci a jihar.

Ya kuma tabbatar wa ƴan jaridar cewa hukumar za ta bada dukkan goyon bayan da ake bukata wurin dakile ayyukan barna a jihar.

EFCC ta gargadi barayin gwamnati

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta ja kunnen masu yiwa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa domin sun shirya daukar matakan da suka dace.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede da ya yi barazanar ba za su saurarawa dukkanin wadanda aka kama da laifin illata tattalin arzikin kasar nan ba idan aka kama su da dibar kudin gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng