Cutar sankarau ta kashe mutum shida a jihar Bauchi
- Rahotanni sun nuna almajirai shida sun mutu sakamakon kamuwa da cutar sanƙarau a garin Udobo, ƙaramar hukumar Gamawa a Bauchi
- Kantoman ƙaramar hukumar ya ce wasu almajirai biyu na kwance a asibiti yayin da wasu kuma aka sallame su bayan sun warke
- Gwamnatin Bauchi ta bayyana cewa cutar ta ɓarke a kananan hukumomi bakwai amma ana ci gaba da ɗaukar matakan daƙile ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Wata cuta da ake zargin sanƙarau ce ta yi ajalin Almajirai shida a makarantar koyo da haddar Alƙur'ani Mai Girma da ke garin Udobo a ƙaramar hukumar Gamawa, jihar Bauchi.
Shugaban ƙaramar hukumar Gamawa, Nairu Baukura ne ya tabbatar da hakan, inda ya ƙara cewa wasu almajirai biyu na makarantar na kwance a asibiti suna jinya.
A cewarsa, bayan waɗanda cutar sanƙarau ta kashe a maƙarantar Tsangayar, yanzu haka an kwantar da wasu a asibitin haihuwa na Udobo, rahoton Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da Baukura ya gaza tabbatar da adadin waɗanda cutar ta kama, ya bayyana cewa an yi nasarar maganin cutar a jikin wasu da dama kuma har an sallame su.
An tattaro cewa ɓarkewar cutar sanƙarau da aka samu ya yaɗu zuwa makarantun Tsangaya guda uku a ƙaramar hukumar Gamawa.
Wane matakai gwamnatin Bauchi ta ɗauka?
Dangane da lamarin, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi, Rilwanu Mohammed, ya tabbatar da cewa jihar na kokarin shawo kan cutar.
Ya bayyana cewa kananan hukumomi bakwai sun samu rahoton bullar cutar sankarau, kuma an ɗauki mataki ta hanyar keɓewa da kuma yi wa waɗanda suka kamu magani.
Mohammed ya bayyana cewa dukkan majinyatan da suka yi mu’amala da masu ɗauke da cutar ana ba su magunguna don dakile yaduwar cutar.
Sai dai ya koka da karancin alluran rigakafin sanƙarau a duniya, inda ya ce jihar Bauchi ta samu damar yi wa mutane allurar rigakafi a kananan hukumomi biyu ne kaɗai kawo yanzu.
Jami’in kiwon lafiyar ya yi gargadin cewa ana kamuwa da cutar ta hanyar tarurrukan jama’a, yana mai jaddada muhimmancin ɗaukar matakan kariya, Daily Post ta tattaro.
Bauchi zata ci gaba da tallafawa talakawa
A wani rahoton kuma Gwamna Bala Mohammed ya yi alƙawarin cewa zai ci gaba da tallafawa mutane da kayan abinci har bayan watan azumin Ramadan a Bauchi.
Ƙauran Bauchi ya kuma ja hankalin al'ummar musulmi su kaunaci juna kuma su yi koyi da kyawawan ɗabi'un Annabi Muhammad SAW.
Asali: Legit.ng