Jami'an EFCC Sun Waiwayi Ƴan Canji Yayin da Darajar Naira Ke Ƙara Faɗuwa a Najeriya
- Jami'an hukumar EFCC sun waiwayi ƴan canji a kasuwar bayan fage da ke Wuse a birnin tarayya Abuja ranar Talata
- Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar ya tabbatar da cewa jami'an EFCC sun kama wasu mutane yayin da suka kai samame a kasuwar
- Kakakin EFCC na ƙasa, Dele Oyewale, ya ce wannan aiki ne da za su ci gaba da yi yayin da ƙimar Naira ke ƙara faɗuwa a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) sun sake waiwayawa kan ƴan canjin kuɗi a birnin tarayya Abuja ranar Talata.
Dakarun EFCC sun ci gaba da kai samame kan wasu ƴan canji tare da rufe shagunansu yayin da ƙimar Naira ke ci gaba da faɗuwa a kasuwar hada-hadar kuɗi.
Wannan mataki da EFCC ke ɗauka na zuwa ne biyo bayan matakan da gwamnatin tarayya da babban banki CBN ke ɗauka na farfaɗo da darajar kuɗin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan canji ke kawo cikas
Jaridar Daily Trust ta tattaro yadda ayyukan wasu ƴan canji masu yaɗa jita-jita a kasuwar musayar kuɗi ta bayan fage da ma ta intanet ke ƙara lalata kokarin taso da Naira.
A makon jiya kaɗai, hukumar EFCC ta cafke ƴan canji akalla mutum 20 bisa zargin suna taimakawa bata garin da ke koƙarin durkusar da kuɗin ƙasar nan, cewar rahoton Gazettengr.
Da yake zantawa da wakilin jaridar bisa sharaɗin ɓoye sunansa, wani ɗan canji ya tabbatar da cewa jami'an hukumar EFCC sun sake cafke wasu ƴan canji yau Talata.
Ɗan kasuwar hada-hadar kudin wanda ke kasuwancinsa a Wuce 4 da ke Abuja ya ce, "Sun ƙara zuwa nan, sun tafi da wasu mutane."
Meyasa EFCC ke kama ƴan canji?
Da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun hukumar EFCC na ƙasa, Dele Oyewale, ya ce wannan samamen da suka kai wani aiki ne da za a ci gaba da yinsa a kai a kai.
"Zamu ci gaba da kai wannan samame, saboda haka idan kun ga jami'an mu sun isa wurin ba ɓatan kai suka yi ba,"
- Dele Oyewale
Darajar Naira ta kara faɗuwa
A wani rahoton kun ji cewa darajar Dalar Amurka tana ci gaba da karuwa a kasuwar hada-hadar kudi yayin da ta haura zuwa N1,402/$1 a ranar Alhamis
Bayanai daga FMDQ sun nuna cewa, darajar Naira ta ragu da N12 daga N1,390 da aka rufe cinikinta a ranar Talata ta makon da ya gabata.
Asali: Legit.ng