Fasinjoji 16 Sun Rasa Rayukansu a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Enugu
- Wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da wata motar bas mai ɗauke da mutum 18 ya salwantar da ran fasinjoji 16 a jihar Enugu
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar a wata sanarwa da ya fitar ya ce hatsarin ya auku ne bayan motar ta ƙwace ta bugi wata katanga sannan ta kama da wuta
- An samu nasarar ceto mutum biyu daga cikin waɗanda hatsarin ya ritsa da su yayin da aka buƙaci mutane su taimaka da bayanai wajen gano ƴan uwan mamatan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - Aƙalla fasinjoji 16 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da motarsu a jihar Enugu.
Fasinjojin da suka rasu sun haɗa da maza 14 da mata biyu bayan motarsu ta yi karo da wata katanga, sannan ta kama wuta a hanyar Enugu/Opi/Nsukka da yammacin ranar Talata.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafin X na rundunar a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hatsarin motan ya auku
Hatsarin kamar yadda Daniel Ndukwe ya bayyana, ya faru ne a lokacin da wata motar bas mai ɗauke da mutum 18 da ke da lambar Bauchi DAS 215 XA ta afkawa wata katanga sannan ta kama da wuta.
Hatsarin ya yi sanadiyyar rasuwar fasinjoji 16 yayin da aka ceto wasu mutum biyu da ransu.
Kakakin ya ƙara da cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa motar tana cikin tsananin gudu ne kafin daga bisani ta ƙwace ta bugi katangar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Rundunar ƴan sandan jihar Enugu na son sanar da jama’a cewa, wani mummunan hatsarin mota ya auku a ranar, 30 ga watan Afrilu, 2024 da misalin ƙarfe 5:20 na yamma, a Ekwegbe, kan titin Enugu/Opi/Nsukka.
"Hatsarin ya yi sanadiyyar asarar rayukan maza mutum 14 da mata biyu waɗanda suka ƙone ƙurmus."
An nemi taimakon jama'a bayan hatsarin
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Kanayo Uzuegbu, tare da jami'an hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) sun ziyarci wurin da hatsarin ya auku.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"Kwamishinan ƴan sanda na kira ga jama'a da za su iya taimakawa wajen gane fasinjoji ko suke da bayanai kan ƴan uwan mamatan da su zo su ba da bayanai ko su kira waɗannan lambobin 08098880172, 08086671202."
Mutum 12 sun rasu a hatsari
A wani labarin kuma, kun ji cewa an rasa rayukan mutum 12 a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan titin Zariya zuwa Kano.
Mummunan hatsarin wanda a cewar hukumomi ya auku sakamakon gudun da ya wuce ƙima ya yi sanadiyyar raunata wasu mutum 28.
Asali: Legit.ng