Mutane Sama da 250 Sun Sha da Ƙyar Yayin da Jirgi Ya Gamu da Mummunan Hatsari
- Jirgin ruwa ɗauke da kayayyakin miliyoyin Naira ya gamu da hatsari a yankin ƙaramar hukumar Asari-Toru a jihar Ribas
- Sai dai sakamakon ɗaukin gaggawa da rundunar sojojin ruwa suka kai wurin, sun ceto fasinjoji sama da 250 lami lafiya
- Kwamnadan sojoji ya ƙara jaddada buƙatar duk wanda zai yi tafiya a ruwa ya sanya rigar ruwa domin kariya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Jami’an rundunar sojin ruwan Najeriya (NNS) na sashin Pathfinder, a ranar Litinin, sun ceto mutane sama da 250 ciki har da kananan yara daga cikin ruwa.
Hakan ta faru ne bayan wani hatsarin jirgin ruwa na dakon kaya mai suna MV Precious Emmanuel, ya rutsa da mutanen a ruwan Buguma, karamar hukumar Asari-Toru ta jihar Ribas.
Jirgin ruwan na haya ya ɗauko kayayyaki na miliyoyin Naira daga Sangana da ke karamar hukumar Brass a jihar Bayelsa, zuwa jettin Nembe da ke Fatakwal yayin da hatsarin ya afku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda haɗarin jirgin ya afku
Jaridar Leadership ta tattaro cewa jirgin ruwan wanda ke jigilar busasshen kifi, ɗanye, nama, da akwatunan barasa ya gamu da hatsari ne yayin da ya ci karo da wani jirgin.
Da yake jawabi a wurin aikin ceto, kwamandan NNS Pathfinder, Desmond Igbo, ya ce babu wanda ya mutu saboda ɗaukin sojojin ruwa suka kai wurin a kan loƙaci.
Mista Igbo ya jaddada buƙatar masu jiragen ruwa da fasinjoji su riƙa ɗaukar matakan ƙariya, musamman sanya rigar ruwa, rahoton Guardian.
"Hatsarin na faruwa nan take jami'an mu suka dira wurin suka fara aikin ceto. Da taimakon Allah da koƙarin mutanen mu, ko mutum ɗaya ba a samu ya mutu ba kuma babu wanda ya ji rauni.
"Bayan yaƙi da ɓarayin ɗanyen mai da miyagun cikin ruwa, muma a rundunar soji muna ceton rayuka kuma yana ɗaya daga cikin ayyukan mu.
"Kamar yadda kuke gani babu wanda yake rigar ruwa kuma mun jima muna jan kunne cewa duk wanda zai tafiya daga nan zuwa can a rika da sanya rigar ruwa."
An kama mai ginin da ya ruguje
A wani rahoton kuma ƴan sanda sun kama ɗan kwangila da mai ginin da ya rushe a Kuntau, ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano domin gudanar da bincike.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Muhammed Gumel ya ce duk wanda aka gano yana da laifi a rushewar ginin da ya yi ajalin mutum uku za a hukunta shi.
Asali: Legit.ng