Kamfanin Simintin Dangote ya Samu Gaggawabar Ribar N166b a Watanni 3

Kamfanin Simintin Dangote ya Samu Gaggawabar Ribar N166b a Watanni 3

  • Duk da hauhawar farashin siminti da matsin tattalin arziki, kamfanin simintin Dangote ya ce ya samu gaggwabar riba na Biliyoyin Naira
  • A rahoton da kamfanin Dangoten ya fitar, ya nuna ya samu Naira Biliyan ₦166 daga farkon shekarar 2024 zuwa watan Maris kafin fitar da haraji
  • Kamfanin ya ce ya sauya dabaru biyo bayan faduwar darajar Naira, inda ya rika fitar da simintin zuwa kasashen ketare ciki har da Ghana da Kamaru

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos-Kamfanin Dangote ya samu gaggwabar ribar N166bn daga farkon shekarar nan zuwa watan Maris duk da faduwar darajar Naira da sauran kalubale.

Kara karanta wannan

Wahalar man fetur ta jawo tashin farashin motoci da sauran abubuwan hawa

Wannan na zuwa ne bayan tashin gwauron zabo da farashin simintin ya yi daga tsakanin ₦5000-₦6000 zuwa tsakanin ₦10000-₦12000 a watan Fabrairu.

Kamfanin Dangote ya samu ribar ne cikin watannin 3
Kamfanin simintin Dangote ya samu gaggawabar ribar N166bn a Watanni 3 Hoto: Dangote Cement Nigeria PLC
Asali: UGC

A tsakanin watannin nan, kamfanin ya samu riba sosai wanda ya hau da kaso 26.1% a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Premium Times ya bayyana cewa haka kuma kamfanin ya kai manyan motocin siminti bakwai zuwa kasashen Kamaru da Ghana.

"Yadda mu ka samu riba," Dangote

Shugaban kamfanin simintin Dangote, Arvind Pathak ya tabbatar da cewa sun fuskanci kalubale da dama a wannan lokacin biyo bayan ragargajewar farashin Naira.

Amma a cewarsa, wannan bai sa sun yi kasa a gwiwa wajen samo riba ga kamfanin simintin ba.

A rahoton da Nairaland ta wallafa, Arvind Pathak ya ce sun sauya dabara ta hanyar ba da karfi wajen fitar da simintin kasashen waje.

Kara karanta wannan

Bayan matatar man Dangote, wani kamfanin mai ya rage farashin man dizal

Ya ce haka ne ma ya sa su ka samu karin kayan da ake fitarwa daga Najeriya da kaso 87.2%.

A rahoton kamfanin, sun samu gaggwabar ribar Naira Biliyan 166.4, wanda bayan an cire kudin haraji ya koma Naira Biliyan 112.7 biliyan.

Dangote ya kafa tarihi a kasuwanci

Attajirin Dan Kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya kafa tarihi bayan yawan arzikinsa ya karu da Naira Biliyan 760 cikin sa'o'i 24, wanda hakan ya tabbatar masa da matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika.

Mujallar Forbes ta wallafa cewa dukiyar Dangote ta haura Dala Miliyan 853 a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu, 2023, inda ta kai Dala Biliyan17.8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.