An Kama Mutum 2 Yayin Wani Gini Mai Bene Ya Kashe Mutane a Jihar Kano

An Kama Mutum 2 Yayin Wani Gini Mai Bene Ya Kashe Mutane a Jihar Kano

  • Ƴan sanda sun kama ɗan kwangila da mai ginin da ya rushe a Kuntau, ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano domin gudanar da bincike
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar, Muhammed Gumel ya ce duk wanda aka gano yana da laifi a rushewar ginin da ya yi ajalin mutum uku za a hukunta shi
  • CP ya ce binciken farko ya nuna akwai sakaci da kuma amfani da kayan gini mara ƙwari kuma babu amincewar gwamnatin jiha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kaddamar da bincike kan lamarin rushewar gini wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku a jihar.

Wasu leburori uku sun mutu a karshen makon nan bayan da wani gini da ake ginawa ya ruguje a Kuntau da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ana fargabar wasu sun rasu bayan gini ya rufto musu a Kano

Kwamishinan ƴan sanda na Kano, Muhammed Gumel.
Yan sanda sun fara bincike kan abin da ya haddasa rushewar gini a Kano Hoto: Kano police command
Asali: Twitter

Kodinetan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) reshen jihar Kano, Nurudeen Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda The Nation ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mutane uku sun mutu yayin da wasu biyu suka samu raunuka a lokacin da ginin mai hawa biyu ya ruguje," in ji shi.

An tattaro mutane biyar ne aka ceto daga cikin ɓaraguzan ginin kuma jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) suka garzaya da su zuwa asibiti.

Yan sanda sun fara bincike

Amma a ranar Asabar ‘yan sanda suka kama mai ginin bisa zargin yin sakaci da yin amfani da kayayyakin gini marasa inganci wanda ya kai ga rugujewa da asarar rayuka.

Haka nan kuma dakarun ƴan sandan sun cafke ɗan kwangilan da ke kula da aikin ginin a wani yunƙuri na gano musabbabin rushewar ginin.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama matashin da ya haɗa baki da wasu suka yi barazanar sace kawunsa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammed Gumel, ya ce idan har aka same su da laifi a lamarin za a gurfanar da su a gaban kotu, rahoton Guardian.

Gumel, a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce:

"Binciken farko da 'yan sanda suka yi ya nuna rashin inganci a ginin kuma an tsiri yin ginin ba tare da amincewar gwamnatin jiha ba.
"Sakamakon haka, a halin yanzu mai ginin yana hannu yana amsa tambayoyi game da laifuffukan keta dokoki da kuma rashin bin ƙa'idojin gini da gangan."

Tankoki sun kama da wuta

A wani rahoton na daban Motoci aƙalla 100 ne suka ƙone yayin da wasu tankokin fetur suka fashe a cunkoson ababen hawa a titin Gabas-Yamna a Ribas.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun maƙale a cikin motocinsu amma har yanzu ba a gano adadin da suka mutu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262