Mutane da Yawa Sun Mutu Yayin da Tankoki Suka Fashe a Cikin Cunkoson Motoci
- Motoci aƙalla 100 ne suka ƙone yayin da wasu tankokin fetur suka fashe a cunkoson ababen hawa a titin Gabas-Yamna a Ribas
- Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun maƙale a cikin motocinsu amma har yanzu ba a gano adadin da suka mutu ba
- Gobarar ta shafe tsawon sa'o'i tana ci kafin daga bisani manyan motocin kashe wuta su samu nasarar shawo kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Ana fargabar akalla motoci 100 da mutane masu yawa ne suka ƙone yayin da wasu tankokin fetur suka fashe a titin Gabas-Yamma, ƙaramar hukumar Eleme a jihar Ribas.
Lamarin ya faru ne ranar Jumu'a, 26 ga watan Afrilu da daddare kuma ya kawo babban cikas ga matafiya a kan titin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
An tattaro cewa lamarin ya fara ne lokacin da wata tanka maƙare da man fetur ta fashe kuma ta kama da wuta kana ta bazu zuwa wasu tankokin da suka maƙale a cinkoso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma wutar ta bazu zuwa wasu motoci da suka maƙale a cunkoson kan titin, kuma har yanzu ba a san adadin yawan mutanen da suka mutu ba.
Yayin da wasu mutanen yankin suka ce motoci sama da 300 ne suka ƙone, wasu kuma sun tabbatar da ƙirga akalla motoci 100 da suka ƙone, rahoton Leadership.
Ko da yake ba a iya tantance adadin mutanen da abin ya rutsa da su ba, amma majiyoyi sun ce mutane da dama da ke cikin motocinsu ake fargabar wutar ta ƙona su.
Me ya haddasa wannan fashewa?
Majiyoyin sun dora alhakin faruwar lamarin kan tukin ganganci da kuma kamfanin da ke gudanar da aikin sake gina sashin Eleme na titin.
An ce gobarar ta shafe sa’o’i da dama amma daga baya manyan motocin kashe gobara tare da tallafin kamfanin Indoroma Petrochemical ne suka kashe ta.
Wani mazaunin yankin ya ce sau biyu ya ji karar murya daga gidansa tare da ihun neman agaji.
“Na ji wata ƙara mai ƙarfi kusan mintuna 20 da suka wuce, kuma mutane suna ta ihu. Sautin ya fito ne daga yankin kamfanin Petro-Chemical. Don haka da na fito sai na ga hayaki da wuta a can nesa.”
Mutum nawa suka mutu?
Wani mazaunin Fatakwal, Segun Owolabi ya ce:
“Na ga gawarwaki hudu da suka kone, wataƙila wasu mutanen sun yanki daji saboda da yawa sun gudu. Na ga dumbin ababen hawa sun kone, tirela ta kone."
"Akwai yiwuwar gano ƙarin gawarwaki, wannan wane irin bala'i ne, Allah ka mana magani, motoci da yawa sun ƙone."
An kashe kwamanda a Katsina
Rahotanni daga jihar Katsina sun nuna cewa ƴan bindiga sun kashe babban kwamandan sojoji a kauyen Malali, ƙaramar hukumar Kanƙara.
Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Alhamis yayin da yake kan hanyar zuwa kai ɗauki kauyen domin daƙile harin ƴan bindiga.
Asali: Legit.ng