Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Jawo Yawaitar Ayyukan Ta'addanci a Afirika

Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Jawo Yawaitar Ayyukan Ta'addanci a Afirika

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun yawaitar ta'addanci da haƙo ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a nahiyar Afirika
  • Tinubu ya bayyana cewa matsalar na ƙaruwa ne saboda kuɗaɗen ƙasashen waje da ake shigowa da su a cikin nahiyar
  • Ya yi kira ga ƙasashen nahiyar Afirika da su tashi tsaye su haɗa kai domin kawo ƙarshen matsalar wacce aka daɗe ana fama da ita

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan yawaitar ayyukan ta'addanci da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a nahiyar Afirika.

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa kuɗaɗen da ake samowa daga ƙasashen waje su ne suka ƙara iza wutar matsalolin guda biyu da ake fama da su.

Kara karanta wannan

'Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da gurfanar da ƴan ta'addan da ta kama a gaban kotu'

Tinubu ya magantu kan ta'addanci a Afirika
Tinubu ya bude taro kan yaki da ta'addanci a Afirika Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ya yi kira ga ƙasashen duniya da su taimaki nahiyar Afirika shawo kan matsalar saboda sun bada gudunmawa wajen samar da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Tinubu ya bada?

Shugaba Tinubu ya kuma nuna muhimmancin buƙatar ƙasashen Afirika su ƙara ƙarfafa haɗin kai a tsakaninsu domin magance barazanar da ta'addanci ya ke yi wa nahiyar.

Shugaban ƙasan ya yi magana ne a ranar Litinin a wajen buɗe taro na kwana biyu kan magance ta'addanci a nahiyar Afirika, wanda ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya shirya a Abuja.

Tinubu ya yi maganar daukar nauyin ta'addanci

Jawabin na Tinubu na ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokim yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a shafin X.

Tinubu ya yi nuni da cewa kuɗaɗen da ake shigowa da su daga wasu wuraren ne ke ƙara iza wutar haƙo ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba wanda ya rikiɗe ya zama ɗaukar nauyin ta'addanci.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya bayyana abin da ya hana a samu cikakken tsaro a Najeriya

A cewarsa haƙo ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba yanzu ya koma hannun ƴan ta'adda domin samun kuɗaɗe daga ƙasashen waje waɗanda suke amfani da su wajen siyan makamai.

Jonathan ya kawo mafita kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana hanyar da za a samu tsaro a Najeriya.

Jonathan ya bayyana cewa ba za a taɓa samun cikakken tsaro a ƙasar nan ba har sai an samar da ƴan sandan jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng