DHQ: Jerin Sunaye da Hotunan Mutane 97 da Ake Nema Ruwa a Jallo Kan Zargin Ta'addanci a Najeriya

DHQ: Jerin Sunaye da Hotunan Mutane 97 da Ake Nema Ruwa a Jallo Kan Zargin Ta'addanci a Najeriya

  • Hedkwatar tsaron Najeriya ta ayyana neman Simon Ekpa, shugaban tsagin IPOB da wasu mutane 96 ruwa a jallo kan zargin ta'addanci
  • Jerin waɗanda ake neman ruwa a jallo ya ƙunshi sunaye da hotuna daga shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma
  • Waɗanda DHQ ta ayyana nema sun haɗa da ƴan ta'adda da masu tada kayar baya da ke da hannu a tashe-tashen hankulan kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ayyana shugaban tsagin ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar biyafara (IPOB), Simon Ekpa, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

DHQ ta sanya sunan shugaban haramtacciyar ƙungiyar ta ta'addanci IPOB tare da wasu mutane 96 a cikin jerin waɗanda take nema a Najeriya.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin sunayen mutum 9 da ƴan canji 6 da ke ɗaukar nauyin ta'addanci ciki har da abokin Gumi

Simon Ekpa da Sojoji.
Ta'addanci: DHQ ta fitar da sunayen waɗanda take nema ruwa a jallo Hoto: Maduka Chinemelum Ogwueleka/HQ Nigerian Army
Asali: UGC

Waɗanda ake nema ruwa a jallo sun kunshi ƴan ta'adda da masu tada kayar baya da sauransu da ake zargin suna da hannu a matsalar tsaron da ake fama a sassan ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin sunaye da hotunan mutanen ya haɗa da ƴan ta'adda daga Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, da kuma ƴan tada ƙayar baya daga Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Kakakin DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya tabbatar da sunaye da hotunan waɗanda ake neman ranar Jumu'a, 22 ga watan Maris, rahoton Punch.

DHQ na neman mutum 43 a Arewa maso Yamma

Jimullar mutum 43 ne hedkwatar tsaron ta bayyana a matsayin waɗanda take nema ruwa a jallo a Arewa maso Yamma, shiyyar da ke fama da ayyukan ƴan bindiga.

Wasu daga ciki sun haɗa da Alhaji Shingi, Malindi Yakub, Boka, Dogo Gide, Halilu Sububu, Ado Aliero, Bello Turji, Dan Bokkolo, Labi Yadi, Nagala, Saidu Idris, Kachalla Rugga da Sani Gurgu.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Gwamna Uba Sani ya bayyana babbar damuwarsa

Mutum 33 a Arewa maso Gabas

An bayyana neman mutane 33 ruwa a jallo a yankin Arewa maso Gabas, yankin da ke fama da rikicin Boko Haram da kungiyar ta'addanci ISWAP.

Sun haɗa da Abu Zaida; Modu Sulum; Baba Data; Ahmad; Sani Teacher; Baa Sadiq; Abdul Saad; Kaka Abi; Mohammad Khalifa; Umar Tella; Abu Mutahid; Mallam Mohammad; Mallam Tahiru Baga; Uzaiya d Ali Ngule.

DHQ na neman mutun 21 a shiyyoyi 2

DHQ ta ayyana jimillar ‘yan tada kayar baya 21 da ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a yankin Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Mutanen sun haɗa da Simon Ekpa, Chika Edoziem, Egede, Zuma, ThankGod, Gentle; Flavour, Mathew, David Ndubuisi, High Chief Williams Agbor da Ebuka Nwaka.

Sauran sun ƙunshi Friday Ojimka, Obiemesi Chukwudi aka Dan Chuk, David Ezekwem Chidiebube da kuma Amobi Chinonso Okafor da dai sauransu.

Jerin sunayen ƴan ta'adda.
Hotunan waɗanda ake nema ruwa a jallo Hoto: The Punch
Asali: UGC

Yan bindiga sun kashe 21

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari kan bayin Allah suna tsaka da cin kasuwa a yankin ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe mutum 21, ciki har da magajin garin sannan sun sace mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262