'Yan Bindiga Sun Kona Dan Banga Kurmus a Wani Sabon Hari

'Yan Bindiga Sun Kona Dan Banga Kurmus a Wani Sabon Hari

  • Ƴan bindiga sun aikata aikin ta'addanci a jihar Anambra bayan sun halaka wani ɗan banga har lahira
  • Miyagun dai sun kai hari ne a ofishin ƴan sandan da ke Amichi a ƙaramar hukumar Nnewi ta Kudu
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce tana ƙoƙarin ganin ta cafke miyagun da suka aikata ɗanyen aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Wasu ƴan bindiga a jihar Anambra sun kai hari tare da ƙona wani ɗan banga a Nnewi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a garin Awka a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, 2024, cewar rahoton jaridar Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Sace-sace a Kaduna da Borno: An ba Shugaba Tinubu mafita

'Yan bindiga sun kai hari a Anambra
'Yan bindiga sun halaka dan banga a Anambra Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Kakakin ya ce rundunar ta jihar za ta farauto miyagun da suka aikata wannan laifin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

A cewar Ikenga, kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Aderemi Adeoye, ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, wajen farauto ƴan bindigan da suka kai harin, tare da ƙona ofishin ƴan bangan da ke Amichi a ƙaramar hukumar Nnewi ta Kudu.

Ya jajanta wa mutanen garin game da kisan da aka yi wa ɗan bangan a yayin harin, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganowa tare da murƙushe ƴan bindigan da suka kai harin.

Kwamishinan ya yabawa ƙungiyoyin ƴan banga a faɗin jihar bisa jajircewar da suke yi na kare mutane, tare da ba da tabbacin cewa ƴan sanda za su yi duk mai yiwuwa wajen kare su.

Kara karanta wannan

Ana cikin azumi 'yan ta'adda sun kai mummunan hari a jihar Arewa

Ƴan bindiga sun halaka sojoji a Delta

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun yi wa dakarun sojojin Najeriya kwanton ɓauna a jihar Delta.

Ƴan bindigan sun halaka sojoji 22 ciki har da manya guda huɗu bayan sun tare su lokacin da suke kan hanyar dawowa daga wajen kwantar da tarzoma a wani ƙauye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng