An Zargi Sanatan PDP da Yunkurin Juyin Mulki a Majalisa, an Samu Karin Bayani
- Sanata Opeyemi Bamidele daga mazabar Ekiti ta tsakiya ya zargi Sanata Abdul Ningi da yunkurin juyin mulki a majalisar dattawa
- Bamidele ya yi ikirarin cewa Ningi ya zargi majalisar da yin cushe a kasafin 2024 kawai don tunzura 'yan majalisar da bata mata suna
- Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta dakatar da SanataNingi, daga Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku kan kalamansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Sanata Micheal Opeyemi Bamidele daga mazabar Ekiti ta tsakiya ya zargi Sanata Abdul Ningi da yunkurin "juyin mulkin farar hula", bayan ya yi ikirarin cewa an yi cushe a kasafin 2024.
Opeyemi Bamidele ya yi zargin cewa Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya yi yunkurin yi wa shugaban majalisar Godswill Akpabio juyin mulki.
Shugaban masu rinjaye a majalisar ya yi ikirarin cewa Ningi yana kokarin tunzura kungiyar Sanatocin Arewa su yi wa Akpabio juyin mulki, wanda ya karbi mulki daga hannun Ahmad Lawan.
Kalaman Sanata Bamidele a kan Ningi
A cikin wani faifan bidiyo da majalisar dattawa ta wallafa a shafin Facebook, an jiyo Bamidele yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wannan abin da babban yayana, Sanata Abdul Ningi ya shirya ko ya yi niyyar yi, tamkar juyin mulkin farar hula ne wanda kuma bai samu nasara ba.
"Ubangiji ya yi albarka ga duk wadanda suka ware kansu daga kungiyar sanatocin Arewa, domin Ningi ya so ya yi amfani da su domin cin ma kudurinsa."
Kalli bidiyon a kasa:
Me yake faruwa a majalisar dattawa?
A karshen makon da ya gabata, Sanata Abdul Ningi ya yi hira da wani gidan talabijin, inda ya yi zargin cewa an yi cushen biliyoyin Naira a kasafin kudin 2024.
Sai dai 'yan majalisar dattawa ba su dauki wannan zargi na Ningi da wasa ba, inda aka kusa ba hammata iska a zauren majalisar a yau Talata, 12 ga watan Maris.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an tayar da hazo sosai a majalisar, inda ake zargin kungiyar Sanatocin Arewa da Ningi ke jagoranta na shirya wata makarkashiya ne a kan lamarin.
An dakatar da Sanata Abdul Ningi
Legit Hausa ta kuma rahoto cewa a zaman majalisar na yau, aka dakatar da Sanata Abdul Ningi, daga Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku.
Kudurin majalisar ya biyo bayan zargin da Ningi ya yi na cewar an yi cushe Naira tiriliyan 3 a cikin Naira Tiriliyan 28.7 na kasafin kudin 2024.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da dakatar da Mista Ningi bayan da mafi rinjayen sanatoci suka goyi bayan kudirin dakatarwar.
Asali: Legit.ng