Ningi: Majalisa Ta Dauki Mataki Kan Sanatan da Yayi Zargin Cushen N3tr a Kasafin 2024

Ningi: Majalisa Ta Dauki Mataki Kan Sanatan da Yayi Zargin Cushen N3tr a Kasafin 2024

  • Majalisar dattawa ta ɗauki matakin ladabtarwa a kan Sanata Abdul Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta tsakiya
  • Majalisar ta dakatar da sanatan na tsawon wata uku biyo bayan zargin da ya yo cewa an yi cushe a kasafin kuɗin shekarar 2024
  • Tun da farko dai Sanata Jimoh Ibrahim ya gabatar da ƙudurin neman a dakatar da Ningi na tsawon watanni 12

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa a ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio, ta dakatar da Sanata Abdul Ningi bisa zargin da ya yi na yin cushe a kasafin kuɗi na 2024.

An dakatar da Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku bayan wata doguwar mahawarar da aka yi a zauren majalisar, cewar rahoton gidan talabijin na Channels tv.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fayyace gaskiya kan masu zargin Buhari ne ya lalata Najeriya

An dakatar da Sanata Abdul Ningi a majalisa
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Majalisar dattawa ta ladabtar da Sanata Ningi

Wani mamba a kwamitin kasafin kuɗi na majalisar dattawa, Jimoh Ibrahim, ya fara gabatar da ƙudirin dakatar da Ningi na tsawon watanni 12 bisa zargin bada bayanan ƙarya da kawo ruɗani a majalisar tarayya ta ƙasa baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wasu ƴan majalisar kamar irinsu Sanata Asuquo Ekpenyong sun nemi a yi wa kuɗirin Jimoh Ibrahim gyaran fuska, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Ekpenyong, wanda ke wakilatar Kuros Riba ta Kudu, ya buƙaci a rage tsawon lokacin da aka dakatar da Sanata Ningi zuwa watanni shida.

Sanata Abdulfatai Buhari daga Oyo ta Arewa ya buƙaci a rage dakatarwar zuwa watanni uku.

Meyasa aka dakatar da Sanata Abdul Ningi?

Akpabio, wanda ya bayyana laifuffukan Ningi a matsayin "masu girma", ya gudanar da wata ƙuri'a a lokacin da mafi yawan ƴan majalisar suka zaɓi amincewa da dakatar da Ningi na tsawon watanni uku.

Kara karanta wannan

Ramadan: Shugaban majalisa ya fadi abin da Najeriya ta fi bukata a lokacin azumi

A wata hira da ya yi, Ningi ya yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya na gudanar da nau’i biyu na kasafin kuɗin 2024.

A cewarsa, kasafin Naira Tiriliyan 28.7 da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi tare da sanya hannu a kai ya bar yankin Arewa a baya.

Ningi: Fadar shugaban ƙasa ta yi martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta yi martani kan zargin da Sanata Abdul Ningi, ya yi na cewa tana amfani da kasafin kuɗi iri biyu na shekarar 2024.

Bayo Onanuga hadimin Shugaba Tinubu wanda ya fitar da wata sanarwa kan batun, ya bayyana zargin na Sanata Ningi a matsayin surutu ne kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng