"Ana Cikin Tafiya": 'Yan Sanda Sun Yi Magana da Wata Ta Tsunduma Cikin Kogi a Legas
- Rahotanni sun ce wata mata fasinja ta salwantar da ranta ta hanyar yin tsalle ta faɗa cikin kogi daga wani jirgin ruwa da ke tafiya a Legas
- Matar da aka bayyana sunan ta a matsayin Folashade, ta bar wata jaka ɗauke da kwalbar maganin ƙwari, katunan asibiti da wasu magunguna
- Kakakin rundunar ƴan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin mai ban takaici
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Wata mata mai suna Folashade Nimotalahi ta yi tsalle ta faɗa cikin kogi daga wani jirgin ruwa mai tafiya, wanda ya ɗauko fasinjoji daga yankin Igando da ke Legas zuwa jihar Ogun.
Ta yaya matar ta kashe kanta?
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito a ranar Litinin, 11 ga watan Maris, Benjamin Hundeyin, kakakin rundunar ƴan sandan Legas, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, 10 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Hundeyin, matar ta hau jirgin ne a daren ranar Asabar, 9 ga watan Maris, daga tashar jirgin ruwa ta Isuti da ke Igando, zuwa Totowu a jihar Ogun.
Ko da yake har yanzu ba a san dalilin da ya sa ta aikata abin da tayi ba, amma Hundeyin ya ce wani mutum da aka bayyana sunansa Rasaq ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ƴan sandan Igando, a safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Maris, inji rahoton The Cable.
Ƴan sandan Legas sun yi ƙarin bayani
Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa jami’an ceto sun fara neman gawarta yayin da ake ci gaba da bincike domin tuntuɓar ƴan uwanta.
Da yake ƙarin haske, Hundeyin ya ce jami’an ƴan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru, kamar yadda kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A kalamansa:
"Akwai fasinjoji 12 a cikin jirgin. Nan da nan sai matar ta cire rigarta ta faɗa cikin kogin.
"Ta bar jaka guda ɗaya ɗauke da kwalbar maganin ƙwari, katunan asibitin Alimosho da wasu magunguna."
An samu hatsarin jirgin ruwa a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja wanda ya salwantar da rayukan mutane da dama.
Mutanen da ake fargabar sun rasa ransu a dalilin hatsarin jirgin ruwan sun haɗa da mata da ƙananan yara masu yawa.
Asali: Legit.ng