‘Yan Bindiga Sanye da Kayan Sojoji Sun Kashe Mutum 4 a Jihar Imo

‘Yan Bindiga Sanye da Kayan Sojoji Sun Kashe Mutum 4 a Jihar Imo

  • 'Yan bindiga sun kashe mutum hudu tare da raunata wani a yayin wani hari da suka kai garin Abacheke da ke jihar Imo
  • An tattaro cewa 'yan bindigar wadanda suka bad da kamanni cikin kayan sojoji sun farmaki garin akan babura a yammacin ranar Juma'a
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Henry Okoye, ya ce an dawo da zaman lafiya garin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Abacheke, jihar Imo - 'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun kashe akalla mutane hudu a wani Ohaji-Egbema ta jihar Imo.

Wani mazaunin yankin ya ce 'yan bindigar sun farmaki garin kan babura uku a yammacin ranar Juma'a, 8 ga watan Maris, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa masallaci a Kaduna, sun bindige masallata ranar Juma'a

'Yan bindiga sun farmaki al'umma a jihar Imo
‘Yan bindiga sun hallaka mutum hudu a Imo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An tattaro cewa mazauna yankin da dama sun bar garin sakamakon faruwar harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, an harbe mutanen ne a gidajensu lamarin da ya haddasa tashin hankali yayin da mutane suka dunga gudun tsira.

Rundunar 'yan sanda ta yi martani

Kakakin 'yan sandan jihar, Henry Okoye, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce an tabbatar da mutuwar mutanen ne a asibiti.

Okoye ya ce yayin da harbin bindiga ya samu mutum biyar, daya daga cikinsu ya rayu kuma yana samun kulawar likitoci a yanzu haka.

"A ranar 8/03/2024 da misalin karfe 1830hrs, wasu bata gari sun farmaki garin Abacheke, kan babura suna ta harbi kan mai uwa da wahabi inda harbi ya samu mutane biyar.
"A martanin da aka mayar da gaggawa, kwamandan da ke kula da Ohaji Egbema da sauran tawaga sun isa wajen.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutane sama da 15, sun tafka mummunar ɓarna ana dab da azumi a jihar Arewa

"Nan take aka kwashi mutanen zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwar mutum hudu da zuwansu, daya kuma na samun kulawar likitoci a asibitin. Ana ci gaba da gudanar da gagarumin aiki a yankin.
"Yayin da zaman lafiya ya dawo a yanzkin, ana gudanar da gagarumin bincike don zakulo bata garin da ke da alhakin yin wannan aika-aikar sannan a sa su fuskanci doka."

- Kakakin 'yan sanda Okoye

'Yan bindiga sun hallaka mutum 17

A wani labarin kuma, mun ji cewa ƴan bindiga sun halaka mutane 17 yayin da suka kai farmaki kauyen Mbaikyor Mbalom da ke ƙaramar hukumar Gwer a jihar Benuwai.

Wata majiya a cikin al’ummar kauyen ta tabbatar da haka ga jaridar The Cable, ta ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen a daren ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng