Tsadar Rayuwa: Tsohon Gwamna Ya Nemo Mafita Ga 'Yan Najeriya

Tsadar Rayuwa: Tsohon Gwamna Ya Nemo Mafita Ga 'Yan Najeriya

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya ce bai kamata ƴan Najeriya su zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matsalar tattalin arziƙi da ake fama da ita ba
  • Ambode ya ce ba Shugaba Tinubu ne ya jawo wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki a halin yanzu ba
  • Ya buƙaci ƴan Najeriya da su marawa Shugaba Tinubu baya domin ya gyara matsalar tattalin arziƙi a maimakon nuna masa yatsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya buƙaci ƴan Najeriya da su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a cikin halin ƙunci da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Ambode ya ce ba Tinubu ne ya jawo taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar nan ba.

Kara karanta wannan

"A ƙara haƙuri" Abu 1 da aka buƙaci Shugaba Tinubu ya yi domin magance tsadar rayuwa a Najeriya

Ambode ya goyi bayan Tinubu
Akinwumi Ambode ya bukaci 'yan Najeriya su daina zargin Tinubu kan tabarbarewar tattalin arziki Hoto: @AkinwunmiAmbode
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a wajen taron gidauniyar Akinjide Adeosun Foundation (AAF) na shekarar 2024 ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambode ya buƙaci a yi haƙuri da Tinubu

Tsohon gwamnan ya ce ya kamata a wanke Tinubu daga duk wani zargi domin a shirye yake ya gyara matsalar tattalin arziƙin Najeriya.

A kalamansa:

"Halin da ake ciki a yanzu ba laifin shugaban ƙasa ba ne. Amma idan ba mu fahimci hakan ba, za mu fara yin wasan zargi. Muna bukatar mu fuskanci matsalolinmu kai tsaye.
"Babban matsalar shi ne mun gaji da rashin gyara matsalolinmu. Yanzu, mun samu wanda ya ɗaura ɗamara wato Shugaba Tinubu."

Ambode ya ce ƴan Najeriya za su sake yin murmushi idan jama’a suka haɗa kansu waje guda suka fara tunanin nemo mafita, inji rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya tsige tallafin man fetur

A kalamansa:

“Har sai mun yanke shawarar mu haɗa kanmu kan mafitar Najeriya, matsalar rashin tsaro ba za ta gushe ba. Dukkanmu muna a matsayin da zamu marawa shugaban ƙasa baya. Ya kamata mu fara tunanin yin hakan."

'A Ƙara Haƙuri' - Jigon APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC reshen jihar Legas ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Shugaba Tinubu.

Anthony Anthony wanda ya amince ƴan Najeriya na fama da yunwa ya buƙaci a ƙara lokaci ga gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Tags: