Yan Sanda Sun Dakatar da Zanga-Zangar NLC a Borno a Kan Wani Dalili 1 Tak
- Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta dakatar da kungiyar 'yan ƙwadago (NLC) daga gudanar da zanga-zanga a fadin jihar a yau Talata
- Rundunar ta ce tana fargabar tubabbun ƴan Boko Haram da suka yi barazanar komawa daji za su yi yunkurin tarwatsa zanga-zagar
- Sai dai ƙungiyar NLC ta jihar ta zargi ƴan sandan da rashin mutunta yarjejeniyar da suka kulla na ba su damar tattaki na kilo mita uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Borno - Tawagar rundunar yaki da ta'addanci karkashin jagorancin kwamishinan 'yan sanda ta dakatar da zanga-zangar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC a jihar Borno.
Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwar an gudanar da ita ne a fadin kasar a ranar Talata, kuma an fara ta a Borno da karfe 8 na safe amma ‘yan sanda suka dakatar da ita.
Dalilin 'yan sanda na hana da NLC yin zanga-zanga
Kungiyar NLC ta jihar ta zargi ‘yan sanda da rashin mutunta yarjejeniyar da suka kulla a baya na ba su damar yin tattaki na tsawon kilomita biyu ko uku, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar NLC na jihar, Yusuf Inuwa, ya yi magana da mambobin kungiyar da suka yi tururuwa a sakatariyar kungiyar a shirin gudanar da zanga-zangar a Maiduguri.
Inuwa, ya shaida wa ma’aikatan cewa, AIG na rundunar ‘yan sandan shiyya ta 15, Abdu Umar da kuma CP na Borno, Mohammed Yusufu ne suka sanya dokar saboda matsalar tsaro a jihar.
Abin da NLC ta fada wa mambobinta a Borno
Ya sanar da su cewa:
“Rundunar ‘yan sanda ta sanar da mu cewa ta samu rahoton sirri da ke nuni cewa wasu 'yan ta'adda na shirin ta da tarzoma a yayin zanga-zangar.
“Kwanaki biyu zuwa uku da suka gabata, an samu rahoton sirri cewa wasu daga cikin ‘yan Boko Haram da suka mika wuya, suna shirin kutsawa cikin mu, wanda ka iya haifar da tarzoma."
Kungiyar NLC ta yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da yadda gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyoyin da suka kulla a ranar 2 ga Oktoba, 2023, bayan cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng