An Yi Harbe-Harbe Yayin da 'Yan Daba Suka Tare Manyan Motoci, Sun Sace Kayan Abinci a Jihar Arewa

An Yi Harbe-Harbe Yayin da 'Yan Daba Suka Tare Manyan Motoci, Sun Sace Kayan Abinci a Jihar Arewa

  • Ana zargin wasu bata gari da tare manyan motoci dauke da kayan abinci a yankin Suleja da ke jihar Neja
  • An rahoto cewa 'yan daban sun wawushe buhuhunan abinci iri-iri bayan sun tare tirelolin a ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu
  • Sai da sojoji suka yi ta harbi a iska don tarwatsa masu wawar amma dai sun tsere da kayan abinci musamman shinkafa da katan-katan na taliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Niger - Sojoji sun bude wuta a ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, lokacin da wasu da ake zargin 'yan daba ne suka farmaki manyan tireloli cike da kayan abinci a yankin Suleja da ke jihar Neja.

Alhassan Abdullahi, wani da abun ya faru a idonsa, ya bayyana cewa 'yan daba sun toshe tireloli da dama da ke fitowa daga Abuja zuwa Kaduna bayan sun kona tayoyi a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An maida motocin abinci 50 Najeriya, za su shiga kasar Nijar bayan umarnin Tinubu

Bata gari sun wawushe motar kayan abinci
Hoton bai da alaka da labarin an yi amfani da shi don misali ne Hoto: REINNIER KAZE/AFP
Asali: Getty Images

Yadda 'yan daba suka wawushe kayan abinci a Neja

Matashin ya ce an sace buhuhunan kayan abinci iri-iri, musamman shinkafa kafin sojoji su isa wajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi ya ce:

"Sai da sojoji sojoji suka isa wurin suka fara harbin bindiga a iska don tsorata 'yan daban. Amma duk da haka, da yawansu sun tsere da buhuhunan shinkafa da katan-katan na taliya da sauran kayan abinci.
"Mun samu labarin cewa 'yan achaba ma suna shirin yin zanga-zanga. Da sun yi hakan a jiya amma ba mu san me ya hana su ba."

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a fadin kasar wanda ya haifar da zanga-zanga a yankuna daban-daban na kasar, rahoton News Direct.

An wawushe kaya a motar Dangote

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa ana zargin cewa mutane sun tare motar kamfanin Dangote Group, sun yi gaba da kayan abincin da aka kinkimo.

Kara karanta wannan

An cafke mutane 5 da ‘sace’ buhuna 1800 na abincin ‘yan gudun hijira a Kano

Rahoton Aminiya ya ce ana zargin wannan mummunan lamari ya auku ne a jihar Katsina da ke yankin Arewacin Najeriya.

Wani bidiyo ya nuna yadda mutane su ke wawar kayan abincin da kamfanin Dangote wanda ya yi fice a Afrika ya dauko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng