Tinubu vs Akpabio: Akpabio Ya Fadi Wani Babban Rudani da Tsohon Gwamnan CBN Ya Haifar
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta ruɗe kan laifin da za ta tuhumi tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele da shi
- A cewar Akpabio, gwamnatin Tinubu ta gamu da taɓarɓarewar tattalin arziƙi, kuma an gano cewa Emefiele ne ya haddasa hakan
- Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa za a iya tuhumar Emefiele da laifin zagon ƙasa ga tattalin arziƙi, mallakar makamai da kuma buga sabbin takardu ba tare da samun kuɗin shiga ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Port Harcourt, jihar Rivers - Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa, ya ce babbar matsalar tattalin arziƙin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke fuskanta, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ne ya haddasa ta.
A halin yanzu dai gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Tinubu tana tuhumar Emefiele ta hannun hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC bisa wasu zarge-zargen almundahana da zamba.
Baya ga rahoton na EFCC, an bayyana wasu almubazzaranci da kuɗaɗe a ƙarƙashin Emefiele a babban bankin Najeriya da wani mai bincike na musamman da shugaba Tinubu ya naɗa ya yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya faɗi ruɗanin da Emefiele ya haifar
Amma Akpabio, a ranar Lahadi, 18 ga watan Fabrairu, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ba ta san laifin da za ta tuhumi Emefiele da shi ba.
Ya ƙara da cewa tattalin arzikin ƙasar nan ya taɓarɓare lokacin da sabuwar gwamnati ta shigo, kuma tsohon gwamnan bankin na CBN ne ya jawo hakan.
Wani ɓangarenna bayanin nasa na cewa:
"A lokacin da muka shiga duba halin da tattalin arziƙin ƙasar nan ke ciki, abin ya yi muni, kun san tsohon gwamnan babban bankin ƙasar nan, ba mu ma san abin da za mu tuhume shi da shi ba.
"Ko a tuhume shi da laifin yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa, ko a tuhume shi da laifin mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba ko kuma a tuhume shi da buga takardun kuɗi ba tare da samun kuɗin shiga ba. Ban san abin da za mu tuhume shi da shi ba."
Kalli bayanin nasa a nan ƙasa:
Yadda Emefiele Ya Cire $6.3m Daga CBN
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban ma'aikaci a babban bankin Najeriya (CBN), Ogau Michael Onyeka, ya bada shaida kan Emefiele a gaban kotu.
Michael ya gaya wa kotun yadda tsohon gwamnan na CBN ya cire $6.3m daga bankin domin biyan masu sa ido kan zaɓe ƴan ƙasashen waje.
Asali: Legit.ng