Zaki ya kashe mai bashi abinci da ya shafe shekaru 9 yana rainonsa a jami'ar Najeriya

Zaki ya kashe mai bashi abinci da ya shafe shekaru 9 yana rainonsa a jami'ar Najeriya

  • Wani zaki ya halaka ma'aikaci OAU, Olabode Olawuyi, a lambun jami'ar kamar yadda rahotanni suka nuna
  • Abiodun Olanrewaju, mai magana da yawun jami'ar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu
  • A cewar Olanrewaju, zakin ya kai wa Olawuyi hari ne yayin da ya ke bashi abinci, aikin da ya saba yi na fiye da shekaru tara

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Ile - Ife - Rahotanni da ke fitowa daga kafafen watsa labarai sun nuna cewa wani zaki dan shekara 9 ya kashe ma'aikacin Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a lambun dalibai mazu nazarin tsirai.

Sanarwar da mai magana da yawun jami'ar, Abiodun Olarewaju ya fitar ta tabbatar da lamarin, yana mai cewa Olawuyi, kafin rasuwarsa ma'aikacin fasaha ne na sashin kula da dabobbi wanda ya shafe fiye da shekaru 10 yana kula da lambun.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari'ar Musulunci ta yi hukunci kan 'yar Tiktok, Ramlat, ta fadi dalilai

Zaki ya cinye mai bashi abinci a Jami'ar OAU
Zaki mai shekaru 9 ya kashe mai bashi abinci a Jami'ar OAU. Hoto: OAU
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olanrewaju ya ce zakin ya kai wa marigayin hari ne a ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu, yayin da ya ke ba wa zakunan abinci a lambun jami'ar.

Abiodun Olanrewaju, mai magana da yawun jami'ar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu

A cewar Olanrewaju, zakin ya kai wa Olawuyi hari ne yayin da ya ke bashi abinci, aikin da ya saba yi na fiye da shekaru tara

A cewar sanarwar, sauran ma'aikatan jami'ar da ke wurin sunyi iya kokarin ceto mai gidansu amma daban ya riga ya masa babban illa.

Sanarwar ta kara da cewa mahukunta a jami'ar sun tura tawaga wurin iyalan mammacin, yayin da shugaban jami'ar, Farfesa Adebayo Bamire, ya kuma bada umurnin a gudanar da sahihin bincike kan dalilin faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Farfesa ya bayyana kuskuren da Tinubu ya fara tafkawa kafin shiga Aso Villa

An ce Olawuyi ne ya raini zakin na tsawon shekara tara kafin ya kai masa hari sannan ya kashe shi.

Idan za a iya tunawa a 2018, wani zaki a gidan dabobbi mai zaman kansa kusa da Pretoria, babban birnin Afirka ta Kudu, ya kashe wata mata yar shekara 22.

A cewar The Punch, zakin ya kai wa matar hari a kusa da Hammanskraal misalin kilomita 45 arewacin Pretoria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

iiq_pixel