Aiki na shine na biyu mafi wahala a duniya, Gwamnan CBN Cardoso
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa aikinsa ne na biyu mafi wahala a duniya.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke bayyana irin nasarar da matakan gwamnatin tarayya suka haifar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cardoso ya magantu ranar Lahadi a Abuja a yayin bude taron majalisar malaman kirista na katolika na 2024.
An yi wa taron lakaci da, "Waliyyai kan wilayya: abun da ke damun coci-coci a Najeriya"
"Zan cigaba da tuna cewa aikina a kasancewarsa na biyu mafi wahala a fadin duniya, abu ne da bazan taba mantawa da shi ba, " in ji gwannan na CBN.
Cardoso, wanda shi ne shugaban taro, ya bada tabbacin cewa duk da wahalar da ake ciki, akwai moriya a nan gaba.
"A kwanakin nan rahoton CBN ya ce, a cikin satin da ya gabata, kusan dalar Amurka biliyan 1.8 ce ta shiga kasuwa.
"Matukar Najeriya za ta dauki matakan da suka dace, Najeriya za ta fice daga matsin tattalin arziki kuma kasuwar canji za ta daidaita kanta, " in ji shi.
Ya ce kwanan nan babban bankin zai yi tattaunawa ta musamman, wanda zai bata damar daukar karin wasu matakai da za su bunkasa tattalin arziki.
Cardoso ya ce anyi kokari wajen bambanta farashin gwamnati da na bayan fage, ya kara da cewa yanzu ana iya ganin bambancin a fili.
"Akwai canji da aka samu sosai. An samu canjin ne sakamakon matakan gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya, wanda yanzu ana ganin alfanu yadda masu zuba jari suka dawo," in ji shi.
Ya ce daya daga matsalar ciyar da tattalin arziki gaba a Najeriya shine dole ka nemo hanyoyin maimakon barin kasar ta shagala da siyo kaya daga kasar waje.
"Dole mu dogara da kanmu. Abin da yan Najeriya ke ta kira akai kenan tsahon lokaci, amma a zahiri, ba ma son ganin hakan.
"Wani abu kuma, tabbas, dole mu rage kwadayin kayan kasashen waje. Kuma hakan na da alaka da abin da na fada na mu tsaya da kafarmu, saboda daga karshe, duk abin abin mutane ke kwadayi da ke janyo karyewar kudinmu za a rage shigo da shi," in ji Cardoso.
Asali: Legit.ng