Gwamna Zulum Ya Ayyana Yin Azumin Kwana 1 a Borno, Ya Fadi Dalili

Gwamna Zulum Ya Ayyana Yin Azumin Kwana 1 a Borno, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jihar Borno ya ayyana gudanar da azumin kwana ɗaya a faɗin jihar domin neman samun sauƙi daga Allah
  • Farfesa Babagana Umara Zulum ya buƙaci a gudanar da azumin ne domin samun sauƙi kan tsadar kayan abinci da ƙaruwar fashe-fashen nakiyoyi a jihar
  • A yayin azumin wanda za a gudanar a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, gwamnan ya buƙaci mutanen jihar da suka gudanar da adduo'in samun zaman lafiya da arziƙi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta ayyana azumin kwana ɗaya a fadin jihar a ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu, domin neman taimakon Allah kan tsadar kayan abinci da kuma fashe-fashen nakiyoyi a manyan titunan jihar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da gwamnoni sun fara shirin ɗaukar mataki 1 da zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Gwamna Babagana Zulum ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi ga al'ummar jihar a ranar Juma’a, 16 ga watan Fabrairun 2024, cewar rahoton The Punch.

Za a yi azumin kwana 1 a Borno
Gwamna Zulum ya nuna damuwarsa kan wahalhalun da ake sha Hoto: @govborno
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa ya damu matuƙa kan wahalhalun da ake fama da su musamman tsadar kayan abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Zulum ya yi nuni da cewa ya fahimci nauyin da hakan ya ɗora kan iyalai da ɗaiɗaikun mutane.

Wane mataki gwamnatin za ta ɗauka?

Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa na ɗaukar ƙwararan matakai don magance matsalar, rahoton Channels tv ya tabbatar.

A kalamansa:

"Gwamnatinmu tana mai da hankali kan farfaɗo da aikin gona, da niyyar ƙara samar da abinci da kuma rage dogaro da tallafin abinci."

Ya ce gwamnatin jihar za ta zuba hannun jari a kan dabarun noman zamani, da bayar da tallafi ga manoma, da samar da hanyoyin inganta noma.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fadi dalili 1 da ya sa tubabbun mayakan Boko Haram ba za su koma kashe-kashe ba

Yaushe za a yi azumin?

A kalamansa:

"A matsayinmu na masu imani da kuma irin abubuwan da muka gani a baya, ina roƙon mai martaba Shehun Borno, da babban limami, limamai, da ƴan uwa Kirista da al’ummar jihar Borno da su yi azumin kwana ɗaya a ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu 2024.

Ya kuma buƙaci kowa da kowa ya yi addu’ar samun zaman lafiya, arziƙi da ci gaban jihar yayin gudanar da azumi.

Gwamnatin Borno Ta Magantu Kan Tubabbun Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Borno ta yi magana kan sahihancin tubar da tubabbun mayaƙan Boko Haram suka yi.

Gwamnatin ta bayyana cewa tubabban mayaƙan sun yi rantsuwa da Al-Qur'ani mai girma cewa ba za su koma aikata kashe-kashe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng