Rundunar Ƴan Sandan Jihar Bauchi Ta Nuna Bajinta, Ta Samu Gagarumar Nasara
- Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta ti nasarar gano wasu muggana makamai a ƙaramar hukumar Ningi ta jihar
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da gano makaman ya bayyana cewa an binne makaman ne a ƙarƙashin ƙasa
- Makaman da aka gano dai sun haɗa da bingigu guda uku ƙirar AK47, bindiga ƙirar AK49 guda ɗaya da sauran makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi, ta gano tarin wasu bindigu da aka boye a ƙarƙashin ƙasa.
Jaridar Nigerian Tribune ta kawo rahoto cewa rundunar ƴan sandan ta gano bindigun ne a ƙoƙarin da take da nufin tabbatar da tsaro a jihar.
Rundunar ta samu nasarar ƙwato makaman ta hanyar shirinta na tattara bayanan sirri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Ahmed Wakili a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata, ya tabbatar da gano makaman, rahoton Leadership ya tabbatar.
Ta ya ya aka gano makaman?
SP Ahmed ya bayyana cewa bayanai masu inganci da rundunar ta samu sun nuna cewa an ga wata jakar leda da ake zargi a kusa da kogin Chika-Chika, kimanin mita 200 daga babban titin da ke kusa da rukunin Gida-Dubu a ƙaramar hukumar Ningi ta jihar.
Bindigogin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK47 guda uku da AK49 guda ɗaya da kuma jigida guda tara da babu komai a ciki.
Da yake yabawa ƴan sandan, kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Auwal Mohammed Musa, ya buƙaci jami’an da su ci gaba da shirin samo bayanan sirri don cimma manufofin rundunar.
Ƴan Sanda Sun Sheƙe Shugaban Ƴan Bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya a birnin tarayya Abuja, sun samu nasarar halaka wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar mutane.
Jami'an ƴan sandan sun sheƙe ɗan bindigan ne a wani samame da suka kai maɓoyarsa da ke wajen birnin Abuja. Ƴan sandan sun kuma raunata wasu daga cikin yaransa.
Asali: Legit.ng