Aikin Allah: Gwamnan Arewa Ya Shirya Ciyar da Talakawa Abinci Kyauta a Watan Azumin Ramadan

Aikin Allah: Gwamnan Arewa Ya Shirya Ciyar da Talakawa Abinci Kyauta a Watan Azumin Ramadan

  • Dakta Nasir Idris ya shirya rabon abinci kyauta a watan azumin Ramadan mai zuwa a jihar Kebbi
  • Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ɗauki akalla masallaci ɗaya a kowace ƙaramar hukuma domin ciyar da jama'a abinci a Ramadan
  • Ya faɗi wannan shiri ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar wakilan kananan hukumomi biyu ranar Litinin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya yi alkawarin ɗaukar masallaci daya a kowace karamar hukumar jihar domin ciyar da abinci kyauta a cikin watan Ramadan.

Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mutanen kananan hukumomin Arewa da Dandi, wadanda suka kai masa ziyarar godiya yau Litinin, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta ɗauki muhimmin mataki da nufin gyara yadda ake zaɓe a Najeriya

Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi.
Gwamna Idris Ya Shirya Rabon Abinci Kyauta a Watan Azumin Ramadan Hoto: Dr. Nasir Idris
Asali: Facebook

Tawagar wakilan kananan hukumomin biyu sun miƙa godiyarsu ga gwamnan ne bisa nasarar da All Progressives Congress (APC) ta samu a zaɓen cike gurbin da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa mazaɓar ɗan majalisar wakilan tarayya Arewa/Dandi na cikin waɗanda aka karisa zaɓensu ranar Asabar, Punch ta ruwaito.

Dan Allah zamu ciyar da mutane a Ramadan - Ƙauran Gwandu

Da yake jawabi yayin ziyarar, Gwamna Idris ya ce gwamnatinsa zata yi wannan aiki na ciyar da al'umma a watan Ramadan ne ba don komai ba sai don neman yardar Allah.

Ya kuma ƙara da cewa za a raba abincin ne domin cika burin da al'umma suka ɗora kan gwamnatinsa musamman mutane masu karamin ƙarfi da ba su da gata sai Allah.

Su wa za su raba abincin?

Ya kuma yi alkawarin ba zai nada wadanda ba su da amfani ga al’ummarsu a muƙami ba, yana mai cewa: “Kafin mu ba kowa mukami, sai mun gano abin da ya yi wa jama’arsa.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani lauya ya yanke jiki ya faɗi a ƙofar Kotu, Allah ya masa rasuwa

Idris ya jaddada kudirin gwamnatinsa na faɗaɗa ayyukan raya kasa a fadin jihar, inda ya nuna cewa manufar dimokuradiyya ita ce aiwatar da ayyuka da tallafawa al’umma.

Mazauna Kebbi sun nuna farin ciki da wannan yunƙuri na Gwamna Idris, amma da yawa sun bada shawarin a sauƙaƙa wa jama'a su siya da kansu zai fi kyau.

Abdul Salisu, ya shaida wa Legit Hausa cewa wannan abu ne mai kyau musamman a watan azumi, inda ya yi addu'ar Allah ya bai wa gwamna ikon aiwatarwa.

"Wannan taimako ne mai kyau, zai sanya farin ciki a zuƙatan wasu domin ana cikin yanayi ba kaɗan ba, Allah ya ba shi ikon aiwatar da hakan," in ji shi.

Amma wani da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ba su buƙatar wani tallafi, "idan ana son taimaka mana a Kebbi to a rage farashin abinci, mutane da kansu zasu siya."

"Sannan a dawo mana da zaman lafiya mu ci gaba da kasuwancin mu hankali kwance, wannan ne babbar bukatar talaka a yanzu."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fadi babban dalili 1 da ya sa ya dakatar da fitaccen basarake a jiharsa

Gwamna Abba zai gana da Tinubu

A wani rahoton na daban Gwamna Abba ya sha alwashin zuwa wurin Bola Ahmed Tinubu kan matsi da yunwar da mutanen jihar Kano ke ciki.

Abba Kabir Yusuf ya faɗi haka ne yayin ganawarsa da ƴan kasuwa da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: