'Yan Sandan Kano Sun Kama Wata Shugaban Mata Masu Yin Gurasa
- Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano sun kama Fatima Auwal, jagoran mata da suka yi zanga-zanga kan hauhawar farashin fulawa da sauran kayan yin Gurasa
- Rahotanni sun nuna cewa wasu mata biyu da namiji daya ne suka kai wa 'yan sanda korafi kan Fatima suna mai cewa tayi amfani da sunan kungiyar masu Gurasa ta yi zanga-zanga
- A bangarenta, Fatima, wacce shugaban wata karamar kungiyan masu 'yin Gurasa ne ta ce bata yi wani laifi ba kawai sunyi zanga-zangan lumana ne don nuna wa gwamnati rashin jin dadinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan Kano ta kama Fatima Auwal, shugaban mata wasu mata masu yin Gurasa a Kano. 'Yan sandan yankin Jakara ne suka kama ta a ranar Asabar.
Gurasa abinci ne da aka saba amfani da shi a sassan arewacin Najeriya, da ake hada shi da fulawa, yis, sukari da ruwa, Nigerian Tribune ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan za a iya tunawa Fatima ta jagoranci wasu mambobin wurin yin zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu kan karin kudin fulawa a ranar Alhamis da ya gabata.
A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, 'yan sandan sun kama ta ne bayan samun korafi daga wasu mata biyu da namiji daya. Sunyi ikirarin ita ba 'yar kungiyarsu bace kuma ba ta da ikon amfani da sunansu don yin zanga-zanga.
Rahotanni daga bisani sun nuna an sake ta kan beli da yamma bayan wasu sun shiga tsakani amma aka bukaci ta koma ofishin 'yan sandan ranar Lahadi.
Martanin Fatima Auwal kan kamata
Fatima Auwal ta yi mamakin kamata, tana mai cewa zanga-zangan lumana suka yi don neman gwamnati ta duba batun tashin farashin fulawa, daya cikin manyan abubuwan da ake amfani da shi wurin yin gurasa.
Ta yi mamakin yadda bayyana ra'ayinsu cikin lumana zai saka 'yan sanda su kama ta.
Ta yi bayani kamar haka:
"'Yan sandan sun ce wasu mata da namiji sunyi korafin cewa munyi amfani da sunan kungiyarsu yayin zanga-zangan, wanda ba gaskiya bane."
Ta yi karin hasken cewa su masu yin gurasa ne, yayin da wadanda ke korafin masu sayarwa ne, don haka tana mamakin yadda za a ce tana yi musu sojan gona, rahoton Solace Base.
Duk da Fatima Auwal na jagorantan wani karamin kungiya na masu yin gurasa, babban kungiyar masu yin Gurasa ta yi korafi ga 'yan sanda da cewa tana ikirarin itace shugaban kungiyarsu, wacce kuma ba ita bace.
Wadanda suka kai korafi wurin 'yan sanda sun magantu
Hadiyyatulahi Hamisu, ciyaman din kungiyar 'Jakara Junction Gurasa Bakers Multi-Purpose Cooperative Society' ya tabbatar sune suka kai korafin wurin 'yan sanda saboda masu zanga-zangar na amfani da sunansu.
Ya yi bayanin cewa duk da Fatima Auwal na shugabantan wani karamin kungiya, ta yi ikirarin cewa itace shugaban babban kungiyar masu yin gurasan.
Ya ce:
"Abin da muke nema daga gareta shine ta koma kafar watsa labarai ta janye kalamanta."
Batun karin farashin fulawa, ya ce lamari ne na kallubalen tattalin arziki, ba wai abin da ya faru nan take ba.
Asali: Legit.ng