An Shiga Jimami Bayan Wani Abu Mara Dadi Ya Auku a Jihar Katsina

An Shiga Jimami Bayan Wani Abu Mara Dadi Ya Auku a Jihar Katsina

  • Wasu miyagu sun shiga har cikin gida sun halaka wata dattijuwa da jikarta a garin Daura na jihar Katsina
  • Rahotanni sun bayyana cewa tsohuwar mai shekara 90 a duniya an halaka ta ne ta hanyar shaƙe ta
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ƙatsina ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Daura, jihar Katsina - A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne aka kashe wata mata mai suna Hajiya Amina ƴar shekara 90 da jikarta Bilkisu, mai shekara 23 a unguwar Tudun Wada da ke garin Daura a jihar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mummunan lamarin ya faru ne a gidansu da ke bayan Tashar Kudu a Daura.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fadi babban dalili 1 da ya sa ya dakatar da fitaccen basarake a jiharsa

Miyagu sun tafka ta'asa a Katsina
An shiga har gida an halaka dattijuwa da jikarta a Katsina Hoto: Dr Dikko Umaru Radda
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, an shaƙe dattijuwar ne har lahira yayin da aka yanka jikarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin garin Daura ya shaida wa jaridar cewa miyagun sun farka cikin Bilkisu tare da cire ƙodarta, zargin da jaridar ba ta samu tabbatarwa ba.

Rahotanni sun nuna cewa ba da daɗewa ba, wasu matasa sun yi fashi a gidan mutanen inda suka tafi da gidan talabijin ɗinsu na plasma.

Marigayan sun kai rahoton faruwar lamarin ga ƴan sanda amma ana ci gaba da gudanar da bincike a lokacin da aka kashe su.

"An gano talabijin ɗin kuma ana ci gaba da gudanar da bincike lokacin da wannan mummunan abu ya faru. Bincike ne kawai zai nuna ko waɗanda suka saci talabijin ɗin suna da alaƙa kai tsaye ko ta kaikaice da kisan."

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Gwamna Dikko Umar Radda na Katsina ya jajantawa iyalan mamatan da kuma masarautar Daura bisa wannan lamari da ya faru.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An bankado babban sanata mai daukar nauyin ta'addanci a Arewa

Ko da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

ASP Abubakar ya kuma bayyana cewa suna ci gaba gudanar da bincike kan lamarin.

Ƴan Bindiga Sun Sace Ƴan Kai Amarya a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsagerun ƴan bindiga sun sace mata kusan 55 yan raka amarya a titin zuwa Damari, ƙaramar hukumar Sabuwa a Katsina.

Lamarin dai ya auku ne da wajen misalin ƙarfe 8:00 na dare yayin ake raka amaryar zuwa ɗakin aurenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng