Gwamnan PDP Ya Fadi Babban Dalili 1 da Ya Sa Ya Dakatar da Fitaccen Basararake a Jiharsa
- Gwamnatin jihar Oyo ta bayyana dalilinta na dakatar da wani firaccen barsaraken gargajiya a jihar
- Gwamnatin ta bayyana cewa an dakaratar da basaraken ne bisa rahotannin sirri da ke alaƙanta shi da masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a jihar
- Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar ba za ta ɗaga ƙafa ga duk wanda ya saɓa doka ba komai girmansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Prince Dotun Oyelade, ya ce gwamnatin jihar Oyo ba za ta ɗaga ƙafa kan duk wani wanda ya saɓa wa doka ba, komai girmansa.
Oyelade na mayar da martani ne kan dakatarwar da gwamnatin jihar ta yi wa Onido na yankin Ido, Oba Gbolagade Muritala Babalola (Gbadewolu I), a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar The Punch.
Ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki tsauraran matakan don aikewa saƙonni ga waɗanda ke taimaka wa masu aikata laifuka a jihar, yana mai cewa "suna cikin inda bai dace ba a lokacin da bai dace ba."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka dakatar da basaraken?
Musamman kwamishinan ya bayyana cewa an dakatar da Onido ne saboda rahoton sirri da ke alaƙanta shi da masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a ƙaramar hukumar Ido ta jihar, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Da yake magana kan yiwuwar tsige Onido daga karagar mulki lokacin da aka kammala bincike, Oyelade ya ce, "komai na iya faruwa."
Idan ba a manta ba, gwamnatin a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 2 ga watan Fabrairu, 2024, mai dauke da sa hannun kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Hon. Olusegun Olayiwola, ta dakatar da basaraken.
Takardar ta nuna cewa Gwamna Seyi Makinde ya amince da dakatarwar ne a ranar 1 ga watan Fabrairun, 2024.
Makinde Ya Caccaki Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Gwamnan ya nuna mamakinsa kan yadda Atiku ya ƙi kiransa don yi masa jaje kann iftila'in da ya faru a jihar.
Asali: Legit.ng