Tashin Hankali Yayin da Bam Ya Halaka Bayin Allah a Arewa, Bayanai Sun Fito
- An samu asarar rayuka bayan wani tashin bam da ya auku a ƙaramar hukumar Gubio ta jihar Borno
- Shugaban ƙaramar hukumar Gubio wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce mutum shida ne suka rasa ransu a sakamakon tashin bam ɗin
- An yi nuni da cewa wasu ƴan jari-bola ne cikin rashin sani suka adana bam ɗin cikin kayayyakin ƙarafansu ba tare da sanin cewa bam ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Wani bam da ya tashi ya kashe Almajirai huɗu da manyan mutane mutum biyu a ƙaramar hukumar Gubio dake jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta ce da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Gubio, Alhaji Mali Gubio, ya ce lamarin ya faru ne a wani ginin da ba a kammala ba da misalin ƙarfe 11:00 na safe, a ranar Asabar.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Duk mutanen da abin ya shafa sun mutu don haka ba za mu iya sanin ainihin abin da ya faru ba, amma fashewar bam ne a wani gida da aka ajiye ƙarafa.
“An gano gawarwakin Almajirai huɗu da manya mutane mutum biyu, amma ba mu iya tantance gawarwakin manyan mutanen biyu ba da aka gano gawarsu a wurin ba, kuma babu wanda ya zo ɗaukarsu."
Ya ce gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya hana jari-bola a jihar domin hana ɓarnatar da kayayyakin gwamnati a yankunan da ba kowa.
Ya ce mutane da yawa sun yi imanin cewa, ba da saninsu ba ne masu jari-bolan suka tattara tare da adana bam ɗin tare da wasu ƙarafa a ginin da ke kusa da makarantar Alqur’anin (Tsangaya), cewar rahoton jaridar Vanguard.
Zulum Ya Faɗi Ɓarnar da Ƴan Ta'adda Suka Yi a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya bayyana cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun lalata sama da kashi 90 cikin 100 na gidaje a jihar.
Gwamna Zulum ya ce babban abin farin cikin shi ne gwamnan da ya gabace shi da kuma shi kansa sun sake gina sama da kaso 30-40 na gidajen da ƴan ta'addan suka lalata a shekara 12 da suka wuce.
Asali: Legit.ng